Yan Bindiga Sun Tsere Daga Dazuzzuka, Sun Saki Wadanda Suka Sace a Arewa

Yan Bindiga Sun Tsere Daga Dazuzzuka, Sun Saki Wadanda Suka Sace a Arewa

  • Dakarun sojoji na ci gaba da tsefe dazuzzuka tun bayan hare-haren yan bindiga a jihar Neja
  • Yan bindiga sun fara tserewa daga dazuzzukan jihar zuwa jihohin da ke makwabtaka saboda hararo farmakin sojojin
  • Sun sako wasu daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su a yankunan Munya, Kafin Koro da Shiroro

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Niger - Biyo bayan farmakin da sojoji suka kai a dazuzzukan jihar Neja, yan bindiga da dama sun fara tserewa daga dazuzzuka tare da sakin wasu da aka yi garkuwa da su, rahoton Leadership.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar yan sandan jihar Neja ta bayyana cewa babu wani kasurgumin dan bindiga da ya ayyana kansa a matsayin gwamna a jihar.

Yan bindiga sun fara tserewa a neja
An yi amfani da horon don misali ne kawai. Wadanda ke hoton ba su da alaka da batun da ake magana kansa a rahoton. Hoto: Patrick Meinhardt/AFP.
Asali: Getty Images

An sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Neja

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Saki Matar Malamin Addini, Sun Kama Wanda Ya Kai Kudin Fansa a Wata Jihar Arewa

Jaridar Leadership ta rahoto cewa an sako wasu manoma da aka yi garkuwa da su kimanin watanni biyar da suka gabata a yankunan Kaffin Koro, Munya da Shiroro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa yan bindigar wadanda ke hasashen harin biyo bayan hatsarin jirgin sojoji na baya-bayan nan da aka alakanta da kungiyar ta'addanci na Dogo Gide sun fara komawa jihohin da ke makwabtaka.

Wata majiya daga garuguwan da ke kusa da yankin Shiroro inda yan bindigar suka yi ta kai farmaki a cikin makonni uku da suka gabata, sun ce sun daina fitowa cike da karfin gwiwa don gudanar da ayyukansu kamar yadda suka yi a makonnin da suka gabata.

Dan bindiga bai zama gwamna ba a Neja, hukumar yan sanda

A halin da ake ciki, rundunar yan sandan jihar a cikin wata sanarwa daga kakakinta, Wasiu Abiodun, ta ce babu dan bindigar da ya ayyana kansa a matsayin gwamna kamar yadda aka dunga yayatawa a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

"Kyau Iya Kyau": Bidiyon Jarumar Fim Da Biloniyan Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet

Ya ce:

"Hukumar ‘yan sandan jihar Neja na son mayar da martani ga wani labari da ke yawo a wasu kafafen sada zumunta cewa wani shahararren dan bindiga ya ayyana kansa a matsayin gwamna a jihar Neja."
"Hukumarmu na son bayani dalla-dalla cewa labarin karya ne gaba ɗaya, kuma hakan mai yuwuwa ta faru a tunanin wanda ya kirkiro labarin ya rubuta."
“Tawagar jami’an tsaro na hadin gwiwa a jihar tare da taimakon gwamnatin jihar suna aiki tukuru domin magance matsalolin tsaro da ake fuskanta. An girke dakaru a wurare daban-daban."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng