Yanzu Muke Samun Labarin Rasuwar Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Bernard Onyeuko

Yanzu Muke Samun Labarin Rasuwar Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Bernard Onyeuko

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Allah ya yiwa fitaccen tsohon kakakin sojin Najeriya rasuwa a yau Asabar
  • Manjo Janar Bernard ya kasance mai magana da yawun soji na tsawon lokaci kafin ya yi ritaya a shekarar nan
  • Tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya taya dangin mamacin jimami

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - An ruwaito cewa, tsohon daraktan fannin yada labarai na tsaro na Najeriya, Maj-Gen. Bernard Onyeuko ya kwanta dama.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa, Onyeuko ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja a safiyar Asabar 26 ga watan Agusta, bayan kamuwa da sanyi sannan aka garzaya da shi asibiti, inda daga baya ya rasu.

Onyeuko ya yi ritaya daga aikin sojan Najeriya a bisa tilas ne bayan nadin sabbin hafsoshin tsaro na kwanan nan.

Kara karanta wannan

“Budurwarsa Ta Ba Shi Kunya”: Malamin Addini Ya Yi Tsalle Daga Ginin Bene Mai Hawa 2, Ya Mutu a Anambra

Allah ya yiwa tsohon kakakin soji rasuwa
Manjo Janar Bernard kenan, marigayin soja | Hoto: Justus Obodoyibo
Asali: Facebook

Wani makusancin marigayin ya shaida wa PRNigeria cewa, Janar din mai ritaya ya kasance kalau a ranar Juma’a sai kawai ya yi korafin kamuwa da mura, inda aka garzaya dashi asibiti ranar Asabar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Garba Shehu ya yi jimami

Garba Shehu, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana jimaminsa, inda ya kira mamacin a matsayin abokinsa.

Ya rubuta a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter) cewa:

“Karanta labari mai ban tsoro cewa mun yi rashin abokinmu, tsohon kakakin soja, Manjo-Janar Bernard Onyeuko (mai ritaya).
"Allah ya sawwakewa 'yan uwasa da samun juriyar rashinsa, Allah ya jikansa."

Najeriya ta sha rashin manyan jami'anta da suka yi mata hidima a yanayi irin wannan, musamman a shekarun nan na baya-baya.

Tsohon gwamnan soja ya rasu

A wani labarin kuma, kunji yadda muka ruwaito rasuwar tsohon gwamnan jihohin Legas da Imo a zamanin mulkin soja, Rear Admiral Ndubisi Kanu (mai murabus) bayan shafe shekaru 77 a duniya.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Abokiyar huldar Kanu kuma mukusanciyarsa, Mrs Joe Okei-Odumakin ta tabbatar wa The Punch labarin a ranar Laraba.

Kanu, wadda tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Murtala Mohammed ya nada cikin majalisar kolin sojoji a shekarar 1975, daga bisani ya zama mai rajin kare hakkin bil adama bayan barin aikin soja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.