Tsohon Gwamnan Sojan Katsina Yahaya Madaki ya rasu
- Jihar Katsina ta rasa wani tsohon Gwamnan ta Yahaya Madaki
- Gwamnan Jihar Masari ya aika ta’aziyyar wannan babban rashi
- Marigayi Yahaya Madaki ya rike mukamai da dama a Najeriya
Wani labari mai takaici ya zo mana daga Jaridar Daily Trust cewa Jihar Katsina ta rasa wani tsohon Gwamnan ta da yayi mulki a lokacin tsohon Shugaban Kasa Janar Ibrahim Babangida watau Kanal Yahaya Madaki mai ritaya.
An haifi Marigayin ne a Garin Gurara da ke cikin Jihar Neja inda ya zama babban Soja a Kasar, Madaki yana cikin wadanda su ka kifar da Gwamnatin Buhari. Yahaya Madaki yayi Gwamnan ne daga karshen shekarar 1989 zuwa farkon 1992.
KU KARANTA: Wani 'Dan Sanda ya kashe kan sata dalilin zargin sata
Bayan an saka masa da mukami da kuma karin matsayi, Madaki ya sauka daga Gwamna lokacin da Saidu Barda ya ci zaben farar hula a 1992. Daga nan ne Kanal din ya koma Jagorancin Barikin da ke kare Shugaban kasa kafin yayi ritaya.
Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya Yahaya Madaki mukami a Hukumar SEC. Daga baya kuma Marigayi Shugaba ‘Yaradua ya tafi da shi a matsayin ma ba Ministan Birnin Tarayya shawar game da harkokin tsaro a Kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng