Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 23, Sun Kama 137 da Ake Zargin Kasurguman Tsageru Ne, Sun Ceto Mutane 41

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 23, Sun Kama 137 da Ake Zargin Kasurguman Tsageru Ne, Sun Ceto Mutane 41

  • Sojojin Najeriya sun yi nasarar kwato makamai da sauran kayayyakin aikata barna a garin kasar
  • An kama wasu 'yan ta'addan da ke addabar jama'a a bangarori daban-daban na kasar nan, musamman Arewa
  • An kuma hallaka wasu daga cikin ta'addan bayan kwace kayayyakin da suka aikata barna da su a Najeriya

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro a Najeriya ta ce dakarun sojojin sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda 23 a cikin makonni tara, tare da kama 109, da kuma masu garkuwa da mutane biyar, The Nation ta ruwaito.

Ta kuma ce an kama wani mai kai bayanan sirri ga 'yan ta'adda daya da kuma 22 da ake zargin barayin mai ne a cikin tsawon lokaci a fadin kasar.

Darakta mai kula da fannin yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya kara da cewa sojojin sun kuma ceto mutane 41 da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Ware Miliyan 700 Don Biyawa Daliban Kano Kudin Makaranta a BUK

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda
Yadda sojoji suka kashe 'yan ta'adda | Hoto: Defense Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

Irin kayayyakin da aka kwato

Buba ya ce ‘yan ta’adda 231 da iyalansu da suka hada da manya maza 25, manyan mata 63 da yara 143 ne suka mika wuya ga sojoji a yankin Arewa maso Gabas, Daily Post ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa sojojin sun samu nasarar kwato makamai 41 da manyan makamai guda 300 da suka hada da bindigogin AK47 guda 14, bindigar AK49 daya, AK47 guda biyu dauke da harsasai na musamman masu hirman 7.62mm da kuma bindigar PKT guda daya.

Sauran kayayyakin a cewarsa, sun hada da LMG guda daya, bindigogin fanfo guda biyu, bindigogi kiran gida kanana guda biyu, bindigogi manya kiran gida guda uku da dai sauransu.

Sojoji za su ci gaba da aikinsu

Buba ya ce sojoji za su ci gaba da bibiyar kungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke haddasa rashin tsaro da dagulewar zaman lafiya a kasar nan.

Kara karanta wannan

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane 3 Yayin Da Suke Kokarin Karbar Kudin Fansa

Ya ba da tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da yin gyare-gyare wajen tabbatar da isasshen tsaron lafiyar ‘yan kasa da kuma maido da aminci a fadin kasar.

An harbe soha a jihar Edo

A wani labarin, wasu 'yan bindiga da ake tunanin 'yan fashi da makami ne, sun bindige wani soja har lahira a birnin Benin na jihar Edo.

Haka nan kuma 'yan bindigar sun yi nasarar dauke wasu buhuna da ke dauke da makudan kudade bayan aikata danyen aikin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mummunan lamarin dai ya faru ne a ranar Laraba, a kan titin Akpakpava, daidai shatale-tale na farko yayin da sojojin su uku ke yi wa buhunan da ake kyautata zaton na kudi ne rakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.