Juyin Mulkin Nijar: Ba Kasashen Turawa Ke Juya Kungiyar ECOWAS, In Ji Alieu Touray

Juyin Mulkin Nijar: Ba Kasashen Turawa Ke Juya Kungiyar ECOWAS, In Ji Alieu Touray

  • Ƙungiyar ECOWAS ta musanta batun da ake na cewa ita karen farautar turawa ce
  • Ta ce babu wata ƙasar ƙetare da ke yi ma ta katsalandan cikin matakan da take ɗauka
  • Shugaban hukumar ECOWAS Omar Alieu Touray ne ya bayyana hakan a Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar raya tattalin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), ta ce ba Turawa ba ne ke tafiyar da al'amuranta kamar yadda wasu ke iƙirari.

Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma'a a Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Na kasashen Turai ke juya ECOWAS ba
ECOWAS ta ce ba kasashen Turai ke juya ta ba. Hoto: ECOWAS - Cedeao
Asali: Facebook

ECOWAS ta musanta iƙirarin cewa Turawa ke juya ta

Touray ya bayyana cewa mutane da dama na yi wa ECOWAS mummunar fahimta da cewa wasu ƙasashen waje ne ke tafiyar da al'amuranta, inda ya ce hakan kuskure ne.

Kara karanta wannan

Kaico: 'Yan Bindiga Sun Bindige Malamin Addini Har Lahira a Jihar Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ECOWAS ƙungiya ce da ta shafe shekaru 48 suna gabatar da ayyukanta kuma tana gudanar da su a cikin tsari kuma a ƙarƙashin doka da oda.

Ya ƙara da cewa babu wata ƙasa ta ƙetare da ke yi musu katsalandan cikin al'amuranta kuma babban burinta shi ne kiyaye haƙƙoƙin al'ummarta da kuma tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

ECOWAS ba ta ƙaddamar da yaƙi kan jamhuriyar Nijar ba

Touray ya kuma bayyana cewa ƙungiyar ta ECOWAS ba ta ƙaddamar da yaƙi kan al'ummar jamhuriyar Nijar ba kuma ba ta da niyyar yin hakan.

Ya ce shugabannin ƙungiyar sun ɗauki matakan da suka dace ne wajen ganin sun dawo da dimokuraɗiyya a Nijar, ciki kuwa har da amfani da ƙarfin soji idan da buƙatar hakan.

A kwanakin baya ne dai ƙungiyar ta ECOWAS ta umarci dakarunta da su kasance cikin shiri domin tunkarar sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: An Bankado Cewa Ministar Shugaba Tinubu Ba Ta Kammala NYSC Ba

El-Rufai ya shawarci ECOWAS kan amfani da ƙarfin soji a Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan shawarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bai wa ECOWAS, kan amfani da ƙarfin soji da take shirin yi a Nijar.

El-Rufai ya ce faɗa tsakanin Najeriya da jamhuriyar Nijar daidai yake da faɗa tsakanin 'yan uwan juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng