ECOWAS Ta Sake Tura Sako Ga Sojin Nijar, Ta Ce Har Yanzu Lokaci Bai Kure Musu Ba Na Sauya Tunani
- Kungiyar Raya Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ta kara bai wa sojin Nijar wata dama don sauya tunaninsu kan mika mulki
- ECOWAS ta bayyana haka ne a yau Juma’a yayin ganawa da ‘yan jaridu inda ta ce har yanzu lokaci bai kure musu ba
- A bangarensu, sojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar sun ce ba za su mika mulki a yanzu ba har sai bayan shekaru uku a kasar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja – Kungiyar Raya Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce har yanzu sojojin Jamhuriyar Nijar su na da sauran daman sauya ra’ayinsu.
ECOWAS ta bayyana haka ne a yau Juma’a 25 ga watan Agusta a Abuja inda ta ce har yanzu lokaci bai kurewa sojojin juyin mulkin ba.
Meye ECOWAS ta ce game da sojin Nijar?
Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Alieu Touray shi ya bayyana haka yayin ganawa da ‘yan jaridu, cewar Punch.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
“Har yanzu, lokaci bai kure ba ga sojojin Nijar don mayar da mulki ga Bazoum da kuma sauraran muryoyin jama’a.
“Kungiyar ECOWAS ba za ta lamunci yin juyin mulki a ko wace kasa da ke yankin Afirka ta Yamma ba.
“Babban abu mai muhimmanci shi ne himmatuwar kungiyar don dakile juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma.”
Wane gargadi ECOWAS ta yi ga Nijar?
Kungiyar na barazanar afkawa kasar da karfin soji idan ba su mika mulki cikin ruwan sanyi ba ga Shugaba Bazoum, TheCable ta tattaro.
Sojojin sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli kan wasu korafe-korafe.
Har ila yau sojin Nijar sun yi fatali da duk wata barazana ta kungiyar ECOWAS inda su ka yi sabbin nade-nade a gwamnatin.
Bayan haka, sojin Nijar sun sanar da cewa ba za su mika mulki ba har sai bayan shekaru uku tare da barazanar hallaka Bazoum yayin da ECOWAS ta ki amincewa da hakan, Trust Radio ta tattaro.
Hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum na ci gaba da kasancewa a tsare da iyalansa a wani gida tun bayan kifar da gwamnatinsa.
Tinubu Ya Ce Shi Ya Ke Hana Sojin ECOWAS Afkawa Nijar
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana shi ya ke hana ECOWAS afkawa Jamhuriyar Nijar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Tinubu ya ce idan da bai taka musu birki ba, da tuni sun afakwa kasar.
Asali: Legit.ng