Kotu Ta Daure Wasu Mutane 2 A Gidan Kaso Kan Zargin Satar Kayan Motocin Dangote

Kotu Ta Daure Wasu Mutane 2 A Gidan Kaso Kan Zargin Satar Kayan Motocin Dangote

  • Kotun majistare da ke jihar Ogun ta daure wasu da ake zargi da satar kayayyakin motocin kamfanin Dangote har watanni uku
  • Wadanda ake zargin, Emmanuel Choice da Ojuola Akande an daure su ne kan satar kayan da su ka kai Naira dubu 976, 715 daga motoci biyu
  • Alkalin kotun, E. O Idowu bayan sun amince da laifukansu ya daure wadanda ake zargi watanni uku a gidan yari

Jihar Ogun - Kotun majistare da ke zamanta a jihar Ogun ta tasa keyar wasu mutane biyu kan zargin satar kayan motar kamfanini Dangote.

Kotun da ke garin Isabo a karamar hukumar Abeokuta ta Kudu ta daure Emmanuel Choice da Ojuola Akande har tsawon watanni uku.

Kotu ta daure wasu mutum 2 bisa zargin satar kayan motocin Dangote
Kotu Ta Tasa Keyar Wasu Mutane Biyu A Gidan Kaso Kan Zargin Satar Kayan Dangote. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Meye su ka sata a motar Dangote?

Ana zargin wadannan mutane da satar kayan motar kamfanin Dangote da su ka kai Naira 976,715 a jimillar da aka yi na yawan kudaden kayan, kamar yadda Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Emefiele Ya Na Neman Hanyar Sasantawa da Gwamnati Kan ‘Satar’ Naira Biliyan 6

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai gabatar da kara, Lawrence Olu-Balogun ya ce a ranar 22 ga watan Agusta sun sace tayoyi guda shida da gargaren mota guda shida da sauran kayayyaki.

Ya ce jimillar kudaden kayayyakin da suka sacen a motocin biyu ya kai Naira 976,715 mallakin kamfanin Dangote, Opera News ta tattaro.

Meye kotun ta ce kan wadanda ake zargi?

Ya ce abin da wadanda ake zargin su ka aikata na cin amana da kuma sata ya sabawa dokar kasa sashe na 516 da 383 da kundin laifuka sa hukunci.

Dukkan wadanda ake zargin sun amince da aikata laifukan da ake tuhumarsu a kai.

Alkalin kotun, E. O Idowu ya daure wadanda ake zargin watanni uku ba tare da zabin biyan kudin tara ba.

A jihar Ogun har ila yau, jami'an 'yan sanda sun kama wani dan fashi da ya yi ikirarin sifetan 'yan sanda na ba su makamai don aika-aika.

Kara karanta wannan

Diesani Alison-Madueke: Ana Tuhumar Tsohuwar Ministan Jonathan Da Cin Hanci, Yan Sandan Birtaniya Sun Yi Bayani

Kasurgumin Dan Fashi Ya Tona Asirin Wanda Ke Ba Su Makami

A wani labarin, wani kasurgumin dan fashi da makami ya bayyana wanda ke ba su makami don yin fashi.

Dan fashin mai suna Akeem Owonikoko ya ce wani Sifetan 'yan sanda ne mai suna Ola ya ke ba su makamai don aika-aika.

Jami'ar hulda da jama'a na hukumar a jihar, Omotola Odutola ita ta bayyana haka yayin da ta ke hira da 'yan jaridu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel