Umahi: Zan Zauna da Masu Kamfanoni Domin Rage Farashin Siminti

Umahi: Zan Zauna da Masu Kamfanoni Domin Rage Farashin Siminti

  • Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin tattauna wa da masu kamfanonin siminti domin rage farashin kayayyakinsu
  • Ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce mafi akasarin 'yan kwangila sun yi ƙorafin cewa siminti ya fi tsada a Najeriya
  • Ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta shirya ware duk kuɗin da ake buƙata domin gina titunan da zasu kai shekara 50

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya yi alkawarin tattaunawa da kamfanonin da ke kera siminti domin rage farashin kayayyakinsu.

Umahi, tsohon gwamnan jihar Ebonyi ya ɗauki wannan alkawari ne yayin da yake hira a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin ɗin Channels ranar Alhamis.

Ministan ayyuka, David Umahi.
Umahi: Zan Zauna da Masu Kamfanoni Domin Rage Farashin Siminti Hoto: David Nweze Umahi
Asali: Facebook

Ministan ya ce ‘yan kwangila sun koka kan tsadar siminti a kasar nan, inda suka yi ikirarin cewa shigo da shi daga waje ya fi sauƙi da kuma arha.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

Jaridar Vanguard ta haƙaito Umahi na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Zan gudanar da kididdiga tare da su (masu sana’ar siminti) don duba farashin simintin idan muka shigo da shi da kuma kudin da suke ba mu a nan cikin gida Najeriya."
“Mafi yawan ‘yan kwangila sun yi korafin cewa siminti ya fi arha idan aka shigo da shi, amma kuma an hana mu shigo da siminti saboda mu taimaka wa masana’antun siminti na gida."
"Amma ya kamata su riƙa yin abinda ya dace duba da yadda muka ba su fifiko. Muna bukatar yin amfani da fasahar kankare. Zai sa hanyoyinmu su dade na tsawon shekaru 50."

FG ta shirya ware kuɗin gina tituna masu inganci

Umahi ya ƙara da cewa gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a shirye take ta samar da kudade domin gina ingantattun tituna a kasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Gwamnonin APC Ko Na PDP Da Ya Kamata Yan Najeriya Sun Canja

Ministan ya ci gaba da cewa:

"Muna duba duk waɗannan abubuwa. Ta yaya za mu rage farashi? Domin batun farko shi ne kudin ayyukan gini."
"Muna duba alkaluman amma da alama 'yan kwangila da yawa ba su yarda ba, amma zan sa su canza, mu duka injiniyoyi ne."
"Ina gaya musu ribar da zasu samu, zan kare duk abin da suke so su samu amma mu taimaki Najeriya, mu gina hanyar da za ta dore kuma abun farin ciki shi ne gwamnatin Tinubu zata ba da kudin."

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Gwamnonin APC Ko Na PDP Da Ya Kamata Yan Najeriya Sun Canja

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya su canza duk gwamnan da ya gaza yin abinda ake tsammani.

Shugaban ya yi wannan kira ne ranar Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja yayin da yake martani kan buƙatar wasu malaman Addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Ana Wahala: Malamin Addinin Musulunci Ya Roki Gwamna Ya Kawowa Talaka Agaji Bayan Tallata APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262