Yan Bindiga Sun Kai Hari Dakunan Kwanan Dalibai Mata a Jami'ar Jihar Rivers
- Wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki gidan kwanan ɗalibai mata a jami'ar jihar Ribas
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigan sun jikkata wasu ɗalibai mata a harin, lamarin da ya haifar da zanga-zanga
- Kakakin hukumar yan sanda ya ce tuni kwamishina ya umarci a ƙara tura dakaru domin tabbatar da tsaro a harabar jami'ar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Rivers - Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a 'Hostel D' dake jami’ar jihar Ribas da sanyin safiyar Alhamis.
Channels tv ta tattaro cewa maharan sun kai farmaki Hostel din jami'ar, wanda aka ware wa ɗalibai mata zalla, da misalin ƙarfe 2:30 na dare.
Shaidun gani da ido sun ce maharan na ɗauke da bindigogi da adduna, inda suka fasa katangar gidan kwanan dalibai matan kana suka kutsa kai, suka far wa wasu dalibai.
Daya daga cikin daliban, sa'ilin da take nuna raunin da aka ji mata, ta ce ‘yan bindigar sun yanke ta da adda a kafarta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin makarantar ba su ce komai ba kan lamarin, amma an ga motocin jami’an tsaro a cikin gidan kwanan daliban da abin ya shafa.
Ɗalibai sun fara zanga-zanga
A halin da ake ciki dai dalibai sun ɓalle da zanga-zangar taɓarɓarewar tsaro a makarantar bayan wannan farmaki da 'yan bindiga suka kai.
Suna rike da alluna masu rubuce-rubuce daban-daban yayin da kofar makarantar ke kulle, kamar yadda jaridar Vanguard ta tattaro.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, a cikin wata ‘yar gajeruwar sanarwa ta hannun kakakinta, SP Grace Iringe-Koko, ta ce an samar da isasshen tsaro a harabar jami’ar.
Sanarwan ta ce:
“Bayan samun rahoton harin ‘yan fashi da makami da aka kai a dakin kwanan dalibai mata na jami’ar jiha, kwamishina ya umurci kwamandan sashin ayyuka, kwamandan yankin Fatakwal, da DPO na Nkpolu da su tabbatar tsaro a jami’ar."
Wani Jirgi Ya Gamu da Mummunan Hatsari a Jihar Nasarawa
A wani labarin na daban Wani jirgin ruwa da ya ɗauko mutane 19 ya nutse a yankin ƙaramar hukumar Lafia da ke jihar Nasarawa.
Majalisar dokokin jihar ta tabbatar da cewa mutane 12 daga ciki sun rasa rayukansu yayin 7 suka tsira da rayuwarsu.
Asali: Legit.ng