Ni Na ke Hana Kungiyar ECOWAS Aukawa Kasar Nijar da Sojojin Yaki In Ji Bola Tinubu
- ECOWAS ta yi niyyar shiga kasar Nijar tun tuni, amma Bola Ahmed Tinubu ya ce shi ya tsaida ta
- Shugaban Najeriya ya ce kungiyar kasashen yammacin Afrikan ta shirya sojoji da za su dura Nijar
- Tinubu ya shaidawa malaman addini haka a lokacin da su ka gana kafin su koma sulhu a Niamey
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya ce shi ne wanda ya jawo dakarun kungiyar ECOWAS su ka ja baya, ba su kai ga aukawa Jamhuriyyar Nijar ba.
Premium Times ta ce Shugaban Najeriyan ya nuna idan ba domin shi ba, da sojoji sun shiga Nijar da nufin dawo da mulkin farar hula a kasar.
Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi wannan bayani a lokacin da ya zanta da wasu malaman musulunci da ke kokari kawo zaman lafiya.
Kokarin malamai a kasar Nijar
Wadannan malamai na Najeriya sun daurawa kan su nauyin ganin an sasanta a kasar makwabtan ba tare da an yi amfani da makami ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabin da ya yi ranar Alhamis, Tinubu ya nunawa malamai da jagororin addinin halin da ya tsinci kan shi a matsayin shugaban ECOWAS.
Jawabin Shugaba Bola Tinubu
“Ina fama da yanayi mai wahala. Idan ka cire ECOWAS a gefe, wasu mutane za su dauki mataki, wadanda ba su cikin karkashin ikonmu.
Ni ne na ke tsaida wadannan bangarori. Ni na rike kungiyar ECOWAS su ka ja baya."
- Bola Tinubu
Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar da wannan jawabi a daren yau kamar yadda aka kawo rahoto a tashar NTA.
Tinubu bai kama suna ba, amma rahoton ya ce ana zargin shugaban Najeriyan ya na nuni ne ga kasar Faransa mai rundunar sojoji cikin Nijar.
Hambarar da Mohammed Bazoum a Nijar
Tun da aka kifar da Mohammed Bazoum, shugaban Najeriyan da ECOWAS ya nuna ba za su amince da mulkin soja ba, dole a komawa farar hula.
Idan har sulhu ya gagara, Mai girma Tinubu da sauran takwarorinsa sun shirya dakarun ECOWAS da za su yi yaki idan akwai bukatar hakan.
APC ta ci kujerar Majalisa
Lanre Ogunyemi ya yi nasara a kotun sauraron karar zabe, kamar yadda labari ya zo mana dazu, an soke sakamakon zaben da aka yi a farkon bana.
Alkalan kotun karar sun tabbatar da Seyi Sowunmi bai cancanci ya nemi takarar majalisa ba, aka ce ‘dan takaran na APC ne asalin mai kujerar.
Asali: Legit.ng