Shugaba Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Ministan Abuja, Nyesom Wike a Villa

Shugaba Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Ministan Abuja, Nyesom Wike a Villa

  • Bola Ahmed Tinubu da Ministan babban birnin tarayya sun yi ganawar sirri a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis
  • Duk da ba a bayyan dalilin wannan taron ba amma ana hasashen ba zai rasa nasaba da rushewar benen nan da ya faru ba
  • Tun zuwansa matsayin ministan Abuja, Wike ya ɗauki matakai da dama da suka haɗa da haramta saida masara a bakin titi

FCT Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike sun yi wata ganawar sirri a fadar shugaban kasa Aso Villa ranar Alhamis.

Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da ake jimamin benen da ya rushe, wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta, 2023.

Shugaba Tinubu da Ministan Abuja.
Shugaba Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Ministan Abuja, Nyesom Wike a Villa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Wike
Asali: UGC

Jaridar Punch ta tattaro cewa har kawo yanzu ba a bayyana ajendar da manyan shugabannin biyu suka tattauna a wurin taron ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wike Ya Bayar Da Umarnin Cafke Mamallakin Benen Da Ya Rufto a Birnin Tarayya Abuja

Amma ana hasashen wannan ganawa da shugaba Tinubu ya yi da Ministan Abuja, Wike ba zata rasa nasaba da ginin da ya danne mutane da yawa ba ranar Laraba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ibtila'in rugujewar ginin ya yi ajalin mutum biyu yayin da wasu mutane 37 ke kwance a Asibiti suna jinyar raunukan da suka samu, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Ana tamanin tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike zai yi wa shugaban ƙasa bayani kan ibtila'in da ya auku da kuma adadin mutanen da lamarin ya taɓa.

Wike a kujerar Ministan Abuja

Tun bayan rantsar da shi a matsayin sabon ministan Abuja, Nyesom Wike ya lashi takobin gyara babban birnin Najeriya.

Wike, tsohon gwamna tsawon zango biyu kuma jigon PDP, ya buƙaci Daraktoci da sauran ma'aikatan hukumar gudanarwa ta Abuja da su tashi tsaye domin bai zo da wasa ba.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Sauki Ya Zo Yayin Da Tinubu Ya Shirya Siyar Da Litar Gas Naira 250 Madadin Fetur, Ya Tura Bukata Ga 'Yan Najeriya

Haka zalika Wike ya haramta 'yan kananan kasuwancin da ake yi a cikin Anguwanni da kuma bakin titi, daga ciki harda siyar da masara da sauran makamancinsu.

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Manyan Malaman Musulunci a Aso Villa

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya gana da wakilan Malumman addinin Musulunci a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

An tattaro cewa manyan Malumman Musulmai sun sake komawa wurin Tinubu ne domin yi masa bayani kan sakamakon ziyarar da suka kai Jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262