Gwamna Obaseki Ya Caccaki Gwamnatin Tinubu Kan Rashin Tsari Kafin Cire Tallafi A Najeriya
- Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ce ya kadu ganin yadda gwamnatin Bola Tinubu ba ta tsara komai ban a taimakon mutane kafin cire tallafi
- Obaseki ya ce ya fi kowa kasancewa cikin tsoro saboda ya fahimci Tinubu ba shi da wani tsari don taimakawa mutane a cikin halin da su ke ciki
- Ya kuma caccaki Bola Tinubu inda ya ce bai ma san wace hanya zai bi ba don magance matsalolin da ya kawo na wahalhalu ga mutane
Jihar Edo – Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da rashin tsari.
Obaseki ya ce kwata-kwata gwamnatin ba ta shirya komai ba na tabbatar da cewa ta samar da wani tsari kafin cire tallafi, Legit.ng ta tattaro.
Meye gwamnan ya ce game da Tinubu?
Arise News ta ruwaito Obaseki na cewa ya kadu bayan fahimtar cewa gwamnatin Bola Tinubu ba ta tsara komai ba na taimakawa talakawan Najeriya da abin ya fi shafa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke ganawa da ‘yan jaridu a jiya Laraba 23 ga watan Agusta a Benin City.
Ya ce:
“Na kadu matuka ganin mutanen da su ka yi ta kamfen cewa za su cire tallafi amma babu wani tsari na tallafawa mutane bayan haka.
“Ba su san meye za su yi su taimakawa talakawa wadanda cire tallafin zai fi shafa ba a kasa.”
Ya soki tsarin Tinubu na cire tallafi
Obaseki ya ce a tsorace ya ke da gwamnatin Tinubu ganin cewa ba ta da wani tsari na tallafawa mutane bayan cire tallafi.
Gwamnan APC A Jihar Arewa Ya Bayyana Abu Daya Tak Da Ya Kamata Ayi Da Yafi Ba Da Tallafi, Ya Bayyana Dalilai
Ya kara da cewa:
“Ina tsoro ganin irin halin da mu ke ciki a kasar ganin yadda gwamnatin ba ta da wani tsari ko mafita ga wannan masifa da ake ciki wanda ita ta jefa mutane a ciki.”
Yahaya Bello Ya Ce Gyaran Tituna Ya Fi Ba Da Tallafin Kudade
A wani labarin, Gwamna jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana cewa madadin ba ta lokaci da gwamnatoci ke yi na ba da tallafi, ya fi kyau su gyara tituna a kasa.
Bello ya ce idan aka gyara tituna a kasar zai yi saurin rage radadin talauci ga 'yan Najeriya fiye da raba kayan agaji ga mutane.
Asali: Legit.ng