Rashin Aikin Ya Ragu Sosai A Najeriya Da Kaso 4.1 A Farkon 2023, NBS Ta Yi Bayani
- Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS ta fitar da sabon rahoto inda aka samu raguwar rashin aikin yi a Najeriya a farkon 2023
- Hukumar ta ce an samu raguwar rashin aikin yi da kaso 4.1 idan aka kwatanta da 5.3 na karshen shekarar 2022
- Babban Daraktan hukumar, Semiyo Adediran shi ya bayyana haka yayin da ya ke jawabi a lokacin kaddamar da kididdigar a Abuja
FCT, Abuja – Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce rashin aikin yi a Najeriya ya ragu da kashi 4.1 cikin dari a farkon wannan shekara ta 2023.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta fitar da sanarwar cewa rashin aikin yi din ya kai 5.3 a karshen shekarar 2022.
Meye NBS ta ce kan rashin aikin yi?
Babban Daraktan hukumar, Semiyo Adediran shi ya bayyana haka yayin gaddamar da sabon tsari na kididdiga a Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alkaluman a karshen shekarar 2020 sun kai kashi 33.3 cikin dari wanda hukumar ta bayyana a rahotonta, TheCable ta tattaro.
NBS ta fitar da wannan rahoto ne a yau Alhamis 24 ga watan Agusta inda babban daraktan hukumar, Semiyo Adediran ya ce sun yi amfani da tsarin ICLS wurin yin kididdigar.
Sanarwar ta ce:
"Sabon tsarin yin kididdigar ya na mayar da hankali kan yadda yanayin aiki ke sauyawa a cikin kasar.
"Binciken ya duba zango na hudu na shekarar 2022 da kuma farkon zango na 2023.
"Kididdigar na duba manya-manyan ma'auni kamar aiki da kuma rashin aikinyi da sa'o'in da aka yi ana aiki da kuma aiki ba a hukumance ba."
Ta yi bayani kan sabon tsari
Hukumar ta ce sabon tsarin an yi shi ne bisa bin ka'idar kasa da kasa wanda kasashen Nahiyar Afirka kamar su Ghana da Kamaru da Chadi da Benin su ka yi amfani da shi.
Har ila yau, Hukumar ya ce aiki ba a hukumance ba kamar su harkar noma na dauke da kaso 93.5 a zango na hudu na 2020.
Yayin da a farkon zango na 2023 kuma ke dauke da kaso 92.6, kamar yadda Aminiya ta tattaro.
NBS Ta Bayyana Samun Karin Farashin Kaya Da Kaso 12
A wani labarin, Hukumar NBS ta fitar da wani rahoto inda ta ce an samu hauhawan farashin kaya da kashi 12 a watan Yuli.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a ranar 17 ga watan Agusta na shekarar 2020.
Asali: Legit.ng