Mayaka 41 Sun Halaka a Wani Rikici Tsakanin Boko Haram Da ISWAP
- An gwabza wani mummunan faɗa a tsakanin ƴan ta'addan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a jihar Borno
- Mayaƙan ƙungiyoyin na Boko Haram da ISWAP waɗanda yawansu ya kai 41 ne dai suka yi bankwana da duniya a dalilin fafatawar
- A yayin faɗan dai mayaƙan Boko Haram sun fi ji a jiki inda aka halaka kwamandojin ƙungiyar masu yawan gaske
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Borno - Aƙalla mayaƙa 41 na ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka baƙunci lahira bayan faɗa ya ɓarke a tsakaninsu ranar Laraba, a jihar Borno.
An tattaro cewa ƴan ta'addan ISWAP waɗanda suka zo a cikin kwale-kwale masu yawa sun farmaki tsagin Boko Haram na Bakoura Buduma a yankin Duguri cikin ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.
Majiyoyi masu tushe sun gayawa Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa mayaƙa 41 ne suka halaka ciki har da kwamandojin ƙungiyoyin.
An ragargaji mayaƙan Boko Haram
Majiyar ya bayyana cewa ƴan ta'addan ISWAP sun ragargaji ƴan ta'addan Boko Haram, inda suka halaka kwamandojin ƙungiyar masu yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ya lissafo sunayen kwamandojin da suka sheƙe zuwa barzahu sun haɗa da Modu Kayi, Abbah Musa, Isa Muhammed, Ibrahim Ali, Kanai Zakariya, Bula Salam, Isuhu Alhaji Umaru, Dogo Salman da Abdulrahman Malam Musa da sauransu.
Ana yawan fafatawa tsakanin Boko Haram da ISWAP
Ana yawan samun fafatawa a tsakanin mayaƙan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP. Ƙungiyoyin na yawan fafatawa ne musamman a dajin Sambisa na jihar Borno da yankin tafkin Chadi.
Mayaƙan ISWAP su ne ke samun galaba biyo bayan sauya sheƙa da wani Abou Idris, tsohon shugaban kai hare-hare na Boko Haram, wanda ya koma ƙungiyar ISWAP domin yaƙar tsohuwar ƙungiyarsa.
Yan Ta'adda Sun Mika Wuya
A wani labarin na daban kuma, ƴan ta'addan kungiyar Boko Haram sun mika wuya ga rundunar dakarun hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) a jihar Borno.
Ƴan ta'addan wadanda suka hada da kwamandoji 4 da mayaka 13 tare da iyalansu 45 ne suka mika wuya ga dakarun sojojin. Ƴan ta'addan sun miƙa wuya ne bayan sojoji sun addabe su da hare-hare.
Asali: Legit.ng