Wani Makeken Ginin Bene Ya Rufto a Birnin Tarayya Abuja

Wani Makeken Ginin Bene Ya Rufto a Birnin Tarayya Abuja

  • Wani ginin bene mai hawa biyu ya rufto a birnin tarayya Abuja ana tsaka da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya
  • Ginin benen dai ya rufto ne cikin tsakar dare inda ya ritsa da mutane masu yawa a cikinsa bayan ya rufto
  • An ceto mutum 37 waɗanda suka maƙale a cikin ɓuraguzan ginin yayin da ake cigaba da ƙoƙarin ceto ragowar mutanen da suka maƙale

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Ana fargabar mutane da dama sun rasu yayin da wasu da dama suka maƙale a cikin wani ginin bene da ya rufto, a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranar Laraba da daddare a birnin tarayya Abuja.

Ginin dai yana a kan layin Lagos Street a yankin ƙauyen Garki na gundumar Garki II a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wike Ya Haramta Sayar Da Gasashen Masara a Abuja, Ya Ba Da Dalili

Wani ginin bene ya rufto a Abuja
Ginin benen dauke yake da gidaje masu yawa Hoto: Leadership.com
Asali: UGC

Wani shaidar ganau ba jiyau ba, Tanko Dabo, wanda ya je wurin bayan ruftowar ginin, ya bayyana cewa benen ɗauke yake da gidaje masu yawa sannan ƙasansa kuma cike yake da shaguna.

Ya bayyana cewa ginin ya rufto ne lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da misalin ƙarfe 11:50 na daren ranar Laraba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"An yi ta jin ƙarar kuka ta ko ina a wajen bayan ginin ya rufto. Akwai mutane da dama waɗanda ko dai sun mutu ko kuma sun maƙale a ciki saboda ginin cike yake da mutane." A cewarsa.

An tabbatar da aukuwar lamarin

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin da misalin ƙarfe 2:00 na dare a shafinsa na Facebook, Ikharo Attah, tsohon hadimin ministan birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa an ceto mutum 37 a cikin ɓuraguzan ginin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Aike Da Sabon Gargadi Ga Wike Da Sauran Ministocinsa

Attah ya bayyana cewa masu aikin ceto na ƙoƙarin ganin sun ceto mutanen da suka maƙale. 

Ya ƙara da cewa wasu mutum biyu da suka samu munanan raunika cikin waɗanda aka ceto ɗin, an garzaya da su zuwa asibiti.

A kalamansa:

"Ya zuwa yanzu an garzaya da mutum 37 da aka ceto zuwa asibiti, mutum biyu daga ciki sun samu munanan raunika. Sauran mutanen na maƙale a ciki, masu aikin ceto da sauran mutane suna wajen."
"Ana cigaba da ƙoƙarin ceto mutanen amma aikin ba ya yin sauri saboda ruwan saman da ake yi. Suna bakin ƙoƙarinsu domin ganin sun ceto mutanen da ke maƙale cikin ɓuraguzan."

Wike Ya Bayyana Masu Kawo Rashin Tsaro a Abuja

A wani labarin kuma, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya haramta siyar da masara a birnin tarayya Abuja.

Wike ya bayyana cewa masu siyar da masara da sauran abubuwa a bakin titi a birnin na daga cikin waɗanda ke janyo matsalar tsaro a birnin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng