Bidiyon Wata Mata Yar Tsurut Tana Tafiya Tare Da Wani Dogon Mutum Ya Bar Mutane Baki Bude

Bidiyon Wata Mata Yar Tsurut Tana Tafiya Tare Da Wani Dogon Mutum Ya Bar Mutane Baki Bude

  • An gano wata mata yar tsurut tana tafiya a titi tare da wani mutum da ya fi ta tsawo nesa ba kusa ba kuma bidiyon ya yadu a TikTok
  • Matashiyar ta hadu matuka amma yanayin kankantar jikinta yasa aka yi saurin lura da ita kuma bidiyon ya haddasa cece-kuce
  • Ba a sani ba ko mata da miji ne su, amma dai an gano su sanye da tufafi iri daya kuma mutane sun kalla cike da mamaki

An gano wata mata yar tsurut tana tafiya a titi tare da wani dogon mutum.

Ajoke Ade ce ta dauki bidiyon matashiyar da mutumin sannan ta yada shi a dandalin TikTok.

Matashiya yar tsurut tare da wani dogon mutum
Bidiyon Wata Mata Yar Tsurut Tana Tafiya Tare Da Wani Dogon Mutum Ya Bar Mutane Baki Bude Hoto: TikTok/@ajokeade423.
Asali: TikTok

Matashiyar matar na da dan karamin jiki, kuma an gano ta tana tafiya tare da mutumin da ya fi ta tsawo nesa ba kusa ba.

Kara karanta wannan

Mai Da Tsohuwa Yarinya: Yadda Mai Kwalliya Ta Sauya Fuskar Yar Shekaru 81 Ta Zama Tamkar Matashiya, Bidiyon Ya Yadu

Ita da mutumin suna sanye da kaya iri daya, amma ba a tabbatar da ko ma'aurata bane su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon wata yar gajeriyar mata ya yadu

Mutanen da suka gansu sun kalle su cike da mamaki yayin da aka ga wani mutum ya dauki wayarsa yana daukarsu bidiyo.

Da aka wallafa bidiyon a TikTok, mutane da dama da suka ga matar sun ce tana da kyau matuka.

Wasu sun ce kankatar jikinta bai rage ta da komai ba ta bangaren kyau.

Kalli bidiyon a kasa:

Yan TikTok sun yi martani ga bidiyon wata mata yar tsurut

@Abdul Bash ya ce:

"Magana ta gaskiya tana da kyau!"

@Mhizjoy45 ta yi martani:

"Mutum bai da sirrinsa a kasar nan kuma."

@bella wealth ta ce:

"Tana da kyau, na so yadda take murmushi."

@Fola Sayomi ta ce:

Kara karanta wannan

Wata Bahaushiya Ta Tashi Kan Mutane Da Sigar Rawanta a Wajen Biki, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

"Ta yaya za ta dauki ciki?"

@sarahshaw134 ta yi martani:

"Tana da kyau faaa."

@High Star ta ce:

"Sune suke sa kayan yara yake tsada ta ko ina."

Matar Kanye West ta sha suka saboda shigar tsaraici da ta yi a Italiya

A wani labari na daban, matar shahararren mawaki Kanye West, Bianca Censori ta haddasa cece-kuce a tafiyar da ma'auratan suka yi zuwa kasar Italiya a kwanan nan.

A cewar TMZ, ma'auratan sun ta yawo a fadin Italiya a cikin watan da ya gabata kuma Bianca bata hango faruwar wani abu ba yayin fitarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng