“Ina Alfahari Da Shi”: Matashi Ya Jinjinawa Mahaifinsa Dan Tsurut, Ya Daura Shi a Kafada

“Ina Alfahari Da Shi”: Matashi Ya Jinjinawa Mahaifinsa Dan Tsurut, Ya Daura Shi a Kafada

  • Wani matashi ya tsuma zukata a soshiyal midiya bayan ya jinjinawa mahaifinsa abun sonsa a ranar iyaye maza na duniya
  • Bidiyon wanda aka wallafa a TikTok ya nuno dan wanda ke cike da alfahari dauke da mahaifinsa a kan kafadarsa
  • Yayin da yake wallafa bidiyon, ya bayyana irin son da yake yi wa mahaifinsa kuma mutane da dama sun yaba masa kan kasancewarsa dan kirki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani dan albarka ya yadu a soshiyal midiya bayan ya jinjinawa mahaifinsa wanda ke da karamin jiki.

Matashin wanda ke amfani da suna @walmart1805 a TikTok ya wallafa bidiyon mahaifinsa a ranar iyaye maza na duniya kuma nan take bidiyon ya yadu.

Uba da dansa
“Ina Alfahari Da Shi”: Matashi Ya Jinjinawa Mahaifinsa Dan Tsurut, Ya Daura Shi a Kafada Hoto: @walmart1805/TikTok.
Asali: TikTok

A bidiyon, an gano mutumin dauke da mahaifin nasa a kafadarsa yana nuna masa soyayya na musamman.

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Ya Nemo Mafita Maimakon Siyan Man Fetur, Ya Mayar Da Janaretonsa Zuwa Mai Amfani Da Iskar Gas a Bidiyo

Koda dai mahaifin nasa ya kasance dan tsurut mai karamin jiki, matashin bai gaji mahaifin nasa ba ta bangaren jiki da tsawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nan take bidiyon ya yadu a soshiyal midiya yayin da mutane da dama suka jinjinawa dan TikTok din kan nunawa duniya mahaifin nasa da ya yi a ranar iyayen maza na duniya cike da alfahari.

Jama'a sun yi martani

@Abena20 ta ce:

"Barka da ranar iyaye maza gare shi. Kai mutumin kirki ne kuma ina kaunarka saboda yadda kake, maza irinka basu da yawa."

@Emmayoger ya yi martani:

"Dan Allah wanene uban a cikinsu wani ya fada mani don Allah."

@OLUWANISOLA_LOVE ya ce:

"Barka da ranar iyaye maza gare shi. Ina ma ace mahaifina na raye. Baka sanin darajar abun da kake da shi sai ka rasa shi. ina alfahari da kai."

@RmF ya yi martani:

Kara karanta wannan

“Aiki Ya Yi Kyau”: Matashi Ya Kammala Hadadden Gidansa, Ya Zuba Kujeru Yan Waje Da Kayan Alatu

"Baaba mahaifiyarka mutuniyar kirki ce, Allah ya albarkace ta, kai da mahaifinka."

@Maryam ta yi martani:

"Allah yasa ya ci riban haihuwarsa."

@Alex ta ce:

"Wanene mahaifin karamin ko dogon."

@Annabel onyekachi 21 ta yi martani:

"Amma wannan yaron baka da ladabi fa kalli yadda ka dauki mahaifinka a kafada."

Matashiya ta nemi auren saurayinta a bainar jama'a, hotuna sun yadu

A wani labari na daban, wata matashiya ta girgiza intanet bayan ta isa gaban saurayinta rike da zoben alkawari.

Matashiyar budurwar dai ta nemi saurayin ya aureta ba tare da la'akari da ko hakan ya saba al'ada ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel