Shugaban Hukumar Sojojin Sama Ya Ziyarci Iyalan Matukan Jirgin Saman Da Suka Yi Hatsari

Shugaban Hukumar Sojojin Sama Ya Ziyarci Iyalan Matukan Jirgin Saman Da Suka Yi Hatsari

  • Shugaban hukumar sojojin saman Najeriya ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan matuƙan jirgin saman hukumar da ya yi hatsari
  • AM Abubakar Hassan ya jajantawa iyalan mamatan kan rashin da suka yi inda ya yi musu alƙawarin ba su duk taimakon da ya dace
  • Shugaban ya bayyana cewa hukumar da ƴan Najeriya ba za su manta da sadaukarwar da jaruman suka yi ba wajen kare ƙasar nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fatakwal, jihar Rivers - Shugaban hukumar sojojin saman Najeriya, AM Hassan Abubakar, ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan matuƙan jirgin sama mai saukar ungulu na MI-171E da ya yi hatsari a jihar Neja, a farkon watan Agusta.

A wata sanarwa da Legit.ng ta samo a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta, AM Abubakar ya ziyarci iyalan matuƙan ne a birnin Fatakwal na jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wata Kungiya Ta Bukaci Ministocin Tinubu Su Yi Murabus, Ta Bayyana Dalilanta

Shugaban NAF ya ziyarci iyalan matukan jirgin da ya yi hatsari
AM Abubakar Hassan ya jajantawa iyalan kan rashin da suka yi Hoto: @NigAirforce
Asali: Twitter

Da yake magana lokacin ziyarar ta'aziyyar, ya bayyana rasuwar matuƙan jirgin a matsayin babbar asara ga hukumar sojojin saman, sannan rashinsu babban giɓi ne ga hukumar.

Shugaban sojojin saman ya tabbatarwa da iyalan cewa hukumar za ta ba su dukkanin gudunmawar da su ke buƙata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

AM Abubakar ya tabbatar musu da cewa sadaukarwar da matuƙan suka yi ba za ta tafi a banza ba, inda ya ƙara da cewa hukumar da sauran ƴan Najeriya za su tuna su a matsayin waɗanda suka bayar da rayuwarsu wajen kare ƙasar nan.

"Hukumar NAF za ta kasance tare da ku da ba ku dukkanin taimakon da ku ke buƙata." A cewarsa.

AM Abubakar ya yaba wa jami'an hukumar

Haka zalika, shugaban hukumar sojojin saman lokacin da yake ganawa da jami'an hukumar, ya yaba musu bisa jajircewar da su ke yi wajen samar da tsaro a yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Hango Wani Sabon Abu Da Zai Faru a Mulkin Shugaba Tinubu

AM Hassan ya bayyana cewa sadaukarwar da takwarorinsu suka yi ba za ta tafi a banza, inda ya ƙara da cewa hukumar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta hana sake aujuwar hakan a nan gaba.

An Yi Jana'izar Matukin Jirgin Sama

A wani labarin kuma, an gudanar da Sallar jana'izar matuƙin jirgin saman da ya yi hatsari a jihar Neja.

An gudanar da jana'izar Flight Lieutenant Ibrahim Adamu Abubakar, a masallacin Haruna Danja cikin garin Zaria na jihar Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng