Kwamishinan 'Yan Sandan Imo Ya Ba Da Umarnin a Kama Sufetan Da Ya Mari Direba a Imo
- Kwamishinan 'yan sandan jihar Imo, ya ba da umarnin a kama wani Sufetan 'yan sanda
- Hakan ya biyo bayan ganinsa da aka yi a cikin wani ɗan gajeren bidiyo yana shararawa wani direba mari
- Tuni dai rundunar 'yan sandan ta yi ram da jami'in domin ya amsa tambayoyi kan abinda ya aikata
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Owerri, jihar Imo - Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, Muhammed Barde, ya ba da umarnin kama wani Sufetan 'yan sandan da ya shararawa wani direba mari.
Hakan ya biyo bayan wani ɗan gajeren bidiyo da ya yaɗu a Intanet, da aka hangi ɗan sandan na shararawa wani mai tuƙa mota tafi kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Sufetan 'yan sandan da ya mari direba ya janyo surutu
Biyo bayan wallafa bidiyon abinda ya faru a kafafen sada zumunta, mutane da dama sun yi tir da abinda ɗan sandan ya yi wa matuƙin motar, inda suka bukaci a hukunta shi.
"Mata masu kwazo": Faifan Bidiyon Zuka-Zukan 'Yan Mata 2 Na Aikin Leburanci Ya Yadu, Mutane Sun Tafka Muhawara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamshinan ta hannun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, ASP Henry Okoye, ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya ce za a binciko jami'in domin hukunta shi.
Daga baya Okoye ya bayyana cewa an kama jami'in da ake zargi da aikata laifin wanda yanzu haka kuma yake amsa tambayoyi kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.
'Yan sanda sun kama matar daga ta kashe jinjirin kishiyarta
A baya Legit.ng ta yi wani rahoto kan matar da rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta kama saboda halaka jinjirin kishiyarta.
An bayyana cewa 'yan sandan jihar Bauchi, sun cafke matar da aka bayyana sunanta da Furera Abubakar, bisa zargin kashe ɗan kishiyarta.
Furera dai ta shiga ɗakin kishiyar ta ta ne da wani maganin kashe ƙwari, wanda da shi ne ta yi amfani wajen halaka jinjirin.
Rundunar 'yan sanda ta haramta zanga-zanga a Kano
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan matakin hana duk wani nau'i na zanga-zanga da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ɗauka a faɗin jihar baki ɗaya.
Matakin na rundunar dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'ya'yan manyan jam'iyyun jihar suka shirya zanga-zanga domin nuna adawa da duk wata murɗiya da suke zargin ana shirin yi a kotun jihar.
Asali: Legit.ng