Faifan Bidiyo Ya Nuna Yadda Kyawawan 'Yan Mata Ke Kwaba Siminti Ya Girgiza Intanet

Faifan Bidiyo Ya Nuna Yadda Kyawawan 'Yan Mata Ke Kwaba Siminti Ya Girgiza Intanet

  • Kyawawan 'yan mata sun girgiza intanet bayan nadar faifan bidiyo su na aikin leburanci ya yadu
  • Cikin kwazo 'yan matan su na kwaba siminti tare da daukar bulok don yabe a jikin gini
  • Mutane da dama sun yabi kwazon 'yan matan yayin da wasu ke korafin yadda matan ke aiki ba takalma

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jama'a sun sha mamaki bayan ganin wasu kyawawan 'yan mata na aikin leburanci a cikin wani faifan bidiyo.

Saboda mafi yawanci maza ne ke irin wannan aikin wahalar amma sai gashi kyawawan 'yan mata na yi.

Faifan Bidiyon Kyawawan'Yan Mata Na Leburanci Ya Girgiza Intanet
Yadda 'Yan Mata Ke Kwaba Siminti Tare Da Aikin Leburanci Ya Girgiza Intanet. Hoto: @chibaby17356.
Asali: TikTok

Bidiyon yadda 'yan matan ke leburanci

A cikin wani faifan bidiyo da aka yada a Tiktok, an gano 'yan matan na kwaba siminti tare da jidon bulok don kai wa wata mai gini.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wike Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Cewa Gwamnonin PDP 10 Sun Gabatarwa Tinubu Da Sunaye Don Ba Su Mukamai

Yayin da ita kuma ta ke amfani da kwababben simintin wurin yabe a jikin gini.

Mutane da dama sun yabi matan yayin da wasu ke korafin cewa 'yan matan ba su saka takalmi ba.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Martanin mutane kan faifan bidiyon.

TEE_MOSES:

"Me yasa ba takalma, idan siminti ya muku illa a gaba ba za ku sake ganin abin daukar hoto ba."

Doublemorny:

"Ubangiji ya taimake ku, ina addu'ar ubangiji ya ba ni mata irinku.

chikwado Umuoba:

"Ba irin mata masu jiran sai saurayinsu ya musu ba."

Evaluv7:

"Hehebeh abin ya kai haka ne, ubangiji ya albarkaci neman ku."

Happilanc:

"Wow, abin mamaki, ubangiji ya albarkaci neman ku."

smart:

"Idan kun ga dama ku gina gidan sama, wanda za ta yi aure za ta yi."

keenydon:

"Ina son haka amma don Allah ku na saka kariya a kafa da hannu, ubangiji ya taimake ku."

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan Ministoci 9 da Zasu Fayyace Nasarar Shugaba Tinubu Ko Gazawa da Dalilai

Budurwa Ta Mayar Da Kyautar Buroshi Na Saurayinta A Shekaru 11

A wani labarin, wata budurwa ta girgiza mutane yayin da ta bayyana abin da saurayinta ya mata cikin shekaru 11 da su ka yi su na soyayya.

Budurwar ta ce duk tsawon tarayyarta da masoyin nata abu uku kadai ya taba shiga tsakaninsu.

Ta ce buroshin goge baki da safa da kuma man gyaran gashi ne kawai ya taba ba ta yayin da ta fusata ta kwashe su don mayar masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel