Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Gano Makaranta Mai Dalibai 5,000 Da Babu Azuzuwa
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bankaɗo wasu matsaloli da suka dabaibaye ɓangaren ilimi a jihar Kano
- Kwamishinan ilimi, Umar Haruna Doguwa, ya ce an gano makaranta mai ɗalibai 5,000 amma babu aji ko banɗaki
- Ya roki majalisar Burtaniya ta kawo ɗauki domin farfaɗo da harkokin ilimi domin gyara goben matasa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ta koka kan yanayin da ta tarad da ɓangaren ilimi a jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa akwai makarantar da ta gano mai ɗalibai 5,000 amma babu azuzuwa da kuma ingantaccen makewayi, rahoton Daily Trust ya tattaro.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, shi ne ya bayyana haka ranar Laraba yayin da ya karɓi bakuncin wakilan Burtaniya a ofishinsa.
Doguwa ya jaddada kudirin gwamnatin Abba na ci gaba da yin aiki kafada da kafada da majalisar Burtaniya domin magance kalubalen da suka dabaibaye fannin ilimi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa jihar Kano na fuskantar manyan kalubalen da ke kawo cikas ga ci gaban ilimi da kuma shafar makomar matasa masu tasowa.
Doguwa ya ce lokaci ya yi da za a farfado da daɗadɗiyar alakar da ke tsakanin gwamnatin Kano da majalisar Burtaniya yayin da jihar ta fara ƙirƙiro da manufofi da tsare-tsare da nufin bunkasa fannin ilimi.
A rahoton jaridar The News, kwamishinan ya ce:
“A Kano yanzu haka muna da makaranta mai dalibai 5,000 babu bandaki, babu azuzuwa da kujeru. Don haka matsalar tana da tsanani da ban tausayi."
“Baya ga wannan, mun samu wata makarantar mai ƙunshe da dalibai 300 amma babu malami ko ɗaya, a lokaci guda kuma ɗaliban suna zama a kan tagogi ko siminti."
Abinda muke buƙata kafin shawo kan matsalar - Doguwa
Doguwa ya bayyana cewa jihar Kano na bukatar kujeru miliyan 1.5 ga daliban makarantun firamare da na gaba da firamare wadanda ƙiyasin kudinsu ya kai biliyoyin naira.
Ya kuma yi nuni cewa tallafin da ake tsammanin majalisar Burtaniya zata kawo Kano yana da yawa, inda ya roƙi majalisar ta taimaka wa gwamnatin Kano wajen shawo kan lamarin.
Hukumar Tace Finafinai Ta Jihar Kano Ta Kulle Sutudiyon Wani Babban Mawaki
A wani rahoton kun ji cewa Hukumar tace fina-finai q Kano ta garƙame sutudiyon mawaƙin siyasa bayan ya yi biris ya ƙi amsa gayyatar da ta yi masa.
Mawaƙin ya bayyana cewa bai san laifin da hukumar take zarginsa da aikatawa ba, duk da wasu rahotanni na cewa ya ɗan taɓa Kwankwaso a waƙa.
Asali: Legit.ng