Shehu Sani Ya Caccaki Tsarin Gwamnatin Tarayya Na Tsamo Mutane Miliyan 133 A Talauci

Shehu Sani Ya Caccaki Tsarin Gwamnatin Tarayya Na Tsamo Mutane Miliyan 133 A Talauci

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya soki alkawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na tsamo mutane daga talauci
  • Sani ya ce kwanan nan mutane za su fara rokon gwamnati ta barsu a cikin talaucin da ta same su
  • Ya ce gwamntin da ta shude ita ma alkawarin da ta yi kenan a baya, yanzu ga wata ma ta yi nata alkawarin

Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya ce nan ba da jimawa ba 'yan Najeriya za su roki a barsu cikin talaucinsu.

Sani ya bayyana haka ne yayin da ya ke martani kan ikirarin da gwamnatin Tarayya ta yi na tsamo 'yan kasar daga talauci.

Shehu Sani ya soki tsarin Gwamnatin Tarayya na tsamo mutane a talauci
Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Shirin Tsamo Mutane Miliyan 133 A Talauci. Hoto: Shehu Sani, Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Meye Sani ya ce kan tsamo mutane a talauci?

Ya ce nan ba da jimawa ba 'yan kasar za su fahimci cewa talaucin da su ka sani ya fi wanda ba su sani ba.

Kara karanta wannan

Matawalle Ya Tura Muhimmin Sako Ga Masu Cece-Kuce A Mukaminsu Na Minista, Ya Ba Da Misali

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a jiya Talata 22 ga watan Agusta.

Ya ce:

"Gwamnatin da ta shude ta yi alkawarin cire mutane a talauci, yanzu ma wannan gwamnatin ta yi alkawarin tsamo 'yan Najeriya a kuncin talauci.
"Muna daf da iso lokacin da mutane za su roki a barsu a talaucinsu.
"Talaucin da ka sani ya fi wanda ba ka sani ba."

Ministar Ma'aikatar Jin Kai Da Walwalar Jama'a, Betta Edu ta ba da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya za ta tsamo mutane miliyan 133 daga talauci.

Meye Edu ta ce kan tsamo mutane a talauci?

Edu ta ce wannan mataki na gwamnatin ya samu goyon bayan Shugaba Bola Tinubu inda ta ce akwai tsare-tsare da za su taimaka don cimma hakan.

Edu ta ce:

"Abin da ya fi muhimmanci shi ne za mu maida hankali wurin tsamo mutane miliyan 133 daga cikin kuncin talauci."

Kara karanta wannan

Wike Ya Jero Mutanen Da Zai Cusa Kafar Wando Daya Da Su Bayan Zama Minista

Da ya ke martani, Shehu Sani ya soki wannan mataki inda ya ce dukkan gwamnatocin biyu alkawarin da su ka yi kenan, cewar Vanguard.

Shehu Sani Ya Soki Tsarin Ba Da Tallafin N8,000

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya soki Shugaba Tinubu kan ba da tallafin Naira dubu takwas inda ya ce wannan kara talauci zai yi.

Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya yi alkawarin bai wa 'yan kasar tallafin rage radadin cire tallafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.