Gwamnatin Delta Ta Rage Wa Ma'aikata Ranakun Aiki Daga 5 Zuwa 3
- Gwamna Sheriff Oborevwori, ya bayyana matakan da ya ɗauka domin rage wa mutane zafin cire tallafin man fetur
- Ya ce gwamnatinsa ta amince da ƙara wa ma'aikata N10,000 domin agaza musu a wannan yanayi da ake fama da shi
- Haka nan gwamnatin Oborevwori ta rage ranakun aiki daga 5 zuwa uku a kowane mako domin taƙaita wahalar zirga-zirga
Delta state - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana matakan da gwamnatinsa ta ɗauka na rage radaɗin cire tallafin man fetur wanda aka jima ana dako a jihar.
Gwamna Oborevwori ya ce gwamnatinsa ta amince da raba ranakun ayyuka ga ma'aikatan jihar Delta, su riƙa zuwa aiki kwanaki uku a kowane mako.
Delta ta amince da ƙara wa ma'aikata N10,000
Ya kuma ce gwamnatinsa ta amince da tallafa wa ma'aikata da ƙarin N10,000 a albashinsu domin su rage ƙarin wahalhalu da tsadar rayuwan da ake fama da ita daga watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana waɗannan matakan ne ranar Talata, 22 ga watan Agusta, 2023 jim kaɗan bayan rantsar da sabbin kwamishinoni.
Kwamishinoni 26 da gwamnan ya naɗa kuma majalisar dokokin jihar Delta ta amince da su sun karɓi rantsuwar kama aiki a gidan gwamnati da ke Asaba, babban birnin jiha.
PM news ta rahoto gwamna Oborevwori yana cewa
"Ma’aikatan da ke matakin aiki na 1 zuwa 14 za a raba musu lokutan aiki zuwa gida biyu, kashi ɗaya za su rika zuwa aiki a ranakun Litinin zuwa Laraba, ɗayan kuma za su fita aiki daga ranar Alhamis zuwa Juma’a.
"Sauran ma'aikatan da suka kai mataki na 15 zuwa sama za su riƙa zuwa ofis yadda ya dace kuma yadda ma'aikatunsu suka ga ya dace su raba musu ayyuka."
Bayan nan kuma gwamnan ya bai wa dukkan sabbin kwamishinonin ma'aikatun da zasu yi aiki bayan rantsar da su a matsayin mambobin majalisar zartarwa.
Shugaba Tunubu Ya Tilastawa Shugaban NIMC Tafiya Hutu
A wani rahoton kuma Bola Tinubu ya tilasata wa shugaban hukumar NIMC, Injiniya Aliyu Abubakar Aziz tafiya hutun dole na watanni uku.
Shugaban ƙasan ya kuma naɗa muƙaddashin shugaban NIMC da kuma shugaban hukumar DTAC na ƙasa.
Asali: Legit.ng