Kotu Ta Yanke Wa Lackara Watanni 6 A Gidan Kaso Saboda Bata Sunan Farfesa A Anambra
- Kotun majistare ta yanke wa wani lakcara, Peter Ekemezie daurin watanni shida a gidan gyaran hali kan zargin bata suna
- Ekemezie na aiki a matsayin lakcara a jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke birnin Awka cikin jihar Anambra
- Ekememzie ya wallafa bayanan karya kan Farfesa Alex Asigbo bayan ya ki amincewa da ba shi bayanai na shaida a kotu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Anambra - Kotu ta yanke wa wani lakcara, Peter Ekemezie da ke jami’ar Nnamdi Azikiwe a jihar Anambra daurin watanni shida a gidan gyaran hali.
Ana zargin Peter da wallafa wasu bayanai da ke dauke da kalmomin bata suna ga wani Farfesa Alex Asigbo.
Meye kotun ke zargin lakcaran?
An daure Ekemezie bisa tuhume-tuhume da su ka hada da bata suna da satar bayanai da kuma zabin biyan tara Naira dubu 300, Daily Trust ta tattaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin yanke hukuncin a kotun majistare da ke Awka babban birnin jihar Anambra, Mai Shari’a, E. C Chukwu ya bukaci wanda ake zargin ya shafe wata daya a asibitin kwakwalwa.
Sannan Mai Shari’a Chukwu ya ba da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali har na tsawon watanni hudu bayan ya gama wata daya a asibitin kwakwalwa, cewar The Sun.
Meye Farfesan ke zargin lakcaran?
Farfesa Asigbo tun farko ya fadawa kotun cewa, Ekemezie ya kwafi sa hannunsa bayan ya ki ba shi bayanan shaida inda ya ba shi shawara da ya nemi takardar sammaci.
Asigbo ya ce wannan shi ya saka Ekemezie rubutawa tare da wallafa bayanan karya a kansa a shafin Facebook, Tori News ta ruwaito.
Ya kara da cewa Ekemezie bayan wallafawa a kafar Facebook ya kuma yada a sauran kafafen sada zumunta.
Har ila yau, har yanzu ba a tabbatar da ko Mista Ekemezie ya na a matsayin lakcara ko kuma sabanin haka ba bayan an yanke masa hukunci.
Lakcara Ya Rasa Aikinsa Kan Zargin Neman Lalata Da Daliba
A wani labarin, wani lakcara a makarantar koyar da aikin jarida ta Najeriya wacce ta ke jihar Legas ya rasa aikinsa kan laifin neman wata daliba da lalata.
Wanda ake zargin, Tene John malami ne a makarantar koyar da aikin jarida wanda aka kora saboda lalata da wata daliba mai suna Anjola Ogunyemi.
Asali: Legit.ng