Labarin Wani Bakano Ya Girgiza WAEC Yayin Da Ya Ci a Guda 9 a Jarrabawar WASSCE
- Masu amfani da kafar sada zumunta sun ba da labarin wani dan Najeriya mai suna Sarki Abba, wanda aka tilasta masa sake rubuta WASSCE a shekarar 1984
- An tattaro cewa hazikin ya samu sakamako mai kyau da makin A guda 9 amma shakkun sakamakon ya shiga zukatan masu shirya jarrabawar
- Bayan ya rubuta jarrabawar a karo na biyu, sai ya bayyana a fili cewa haziki ne na gaske, wannan yasa aka ba shi lambobin yabo da suka kamace shi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Sarki Abba, wani dan jihar Kano, ya bai wa mahukuntan hukumar shirya jarabawa mamaki saboda kwazon da ya nuna a jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE) a 1984 inda ya samu maki 9 gaba daya A.
Bisa shakkun yadda ya yi wa jarrabawar cin kaca, an kawo shi jihar Legas domin sake rubuta jarabawar a karkashin kulawar manyan masana.
Abin ya ba kowa mamaki, Abba ya sake samun makin da ya samu, wanda hakan ya sa hukumomi suka nemi afuwa tare ba shi lambar yabo ta kasa.
Yadda ya yi bajinta a ABU
Abba ya ci gaba da haskakawa a fannin ilimi, inda ya kammala karatunsa a matsayin babban dalibin likitanci da ya fi kowa maki a ABU Zaria a shekarar 1989/90.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga dai abin da farko aka yada a kafar Facebook game da dalibin mai matukar kokari da himma wajen ilimi da nuna kwarewa.
A yanzu haka dai rayuwa ta sauya, ko a ina Abba yake? Wannan kuma wadanda ya rayu da su da kuma aiki ko wai wani abu da ya hada.
Ba sabon abu bane a Arewacin Najeriya da Kudancinta a samu hazikan daliban da ke ba da mamaki a fannin ilimi da ma aiki.
Wani dalibin na daban da ya ba mamaki a ABU
Legit.ng ta samu rahoton wani hazikin dalibi mai kokari daya zamo dalibi mafi hazaka a sashin karatun likitanci na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, ABU.
Wannan dalibi mai suna Suraj Shuaibu ya lashe manyan kyautuka har guda biyar da suka hada da kyautan dalibi mafi hazaka, wanda yafi iya karatun sanin jikin mutum, wanda yafi iya karatun hada magunguna, wanda ya fi iya karatun tiyata da ilimin sanin cututtuka.
Likita Suraj Shuaib dan asalin jihar Jigawa ya zamo darasi ga sauran dalibai inda zasu fahimci cewar muddin dalibi ya dage zai samu bukata.
Asali: Legit.ng