Gwamnan Borno ya kyautata ma dalibi da ya samu maki 364 a JAMB da N5,000,000

Gwamnan Borno ya kyautata ma dalibi da ya samu maki 364 a JAMB da N5,000,000

Hazikin dalibi mai suna Galadima Zakari da ya samu mafi kyawun sakamako a jarabawar JAMB, ya gamu da sha tara na arziki daga gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a ranar Talata, 7 ga watan Agusta.

Legit.ng ta ruwaito dalibi Zakari dan asalin jihar Borno ne, kuma ya nuna bajinta a jarabawar JAMB ta bana, inda ya samu maki dari uku da sittin da hudu, 364, hakan ya sanya shi zama dalibi mafi yawan adadin maki a cikin dubunnan dalibai da suka zana jarabawar.

KU KARANTA: Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindigar jihar Benuwe

Gwamnan Borno ya kyautata ma dalibi da ya samu maki 364 a JAMB da N5,000,000
Zakari

Tuni jami’ar Covenant dake jihar Ogun ta baiwa Zakari gurbin karanta kimiyyar wutar lantarki, amma alherin bai tsaya nan ba, inda Gwamnan jihar Borno ya sanar da daukar nauyinsa tun daga farko har karshen karatun jami’arsa, da za’a kashe masa kudi naira miliyan biyar.

Gwamna Shettima ya bayyana cewa jihar Borno na alfahari da wannan hazikin dalibi, sa’annan ya kara da cewa dukkanin kabakin Arzikin da ya baiwa Zakari na karkashin kulawar ma’aikatar ilimin jihar.

Gwamnan Borno ya kyautata ma dalibi da ya samu maki 364 a JAMB da N5,000,000
Gwamnan Borno

A sanarwar da hukumar JAMB ta fitar a cikin satinnan, cikin dalibai biyar da suka yi zarra a jarabawar JAMB, Zakari ne kawai dalibi daya tilo daga yankin Arewa, kuma shi ya zamo na daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng