Dalibin ABU yayi fice a ɓangaren karatun likitanci, ya lashe lambobin yabo guda 5

Dalibin ABU yayi fice a ɓangaren karatun likitanci, ya lashe lambobin yabo guda 5

- Wani dalibi daga jihar Jigawa ya zamto zakaran gwajin dafi a sashin karatun likitanci na jami'ar ABU

- Dalibin mai suna Suraj Shuaib ya lashe kyaututtuka har guda biyar, fiye da sauran daliban sashin

Legit.ng ta samu rahoton wani hazikin dalibi mai kokari daya zamo dalibi mafi hazaka a sashin karatun likitanci na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, ABU.

Wannan dalibi mai suna Suraj Shuaibu ya lashe manyan kyautuka har guda biyar da suka hada da kyautan dalibi mafi hazaka, wanda yafi iya karatun sanin jikin mutum, wanda yafi iya karatun hada magunguna, wanda ya fi iya karatun tiyata da ilimin sanin cututtuka.

KU KARANTA: Malamin Shi’a ya wanke gwamna El-Rufai kan zargin zagin El-Zakzaky

Likita Suraj Shuaib dan asalin jihar Jigawa ya zamo darasi ga sauran dalibai inda zasu fahimci cewar muddin dalibi ya dage zai samu bukata.

Dalibin ABU yayi fice a ɓangaren karatun likitanci, ya lashe lambobin yabo guda 5
Dakta Suraj Shuaib

Daya daga cikin abokansa ma ya watsa wannan labara a shafinsa na Facebook inda yace

“Alhamdulillah! Ina amfani da wannan dama don in bayyana muku abokina mai kokari, Suraj Shuaibu wanda ya kammala karatun digiri na Likitanci a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

“Suraj dai dan asalin garin Dutse ne, dake jihar Jigawa. Muna alfahari da kai Likita.”

Ga lambobin yabon daya lashe:

Dalibin ABU yayi fice a ɓangaren karatun likitanci, ya lashe lambobin yabo guda 5
Kyautar sanin cututtuka

Dalibin ABU yayi fice a ɓangaren karatun likitanci, ya lashe lambobin yabo guda 5
Kyautar sanin hada magunguna

Dalibin ABU yayi fice a ɓangaren karatun likitanci, ya lashe lambobin yabo guda 5
kyautar dalibin daya ciri tuta

Dalibin ABU yayi fice a ɓangaren karatun likitanci, ya lashe lambobin yabo guda 5
Kyautar sanin jikin mutum

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An karrama yan Najeriya a kasar waje

Asali: Legit.ng

Online view pixel