Gwamna Fintiri Ya Taya Wike Murnar Zama Ministan Birnin Tarayya Abuja

Gwamna Fintiri Ya Taya Wike Murnar Zama Ministan Birnin Tarayya Abuja

  • A ranar Litinin, 21 ga watan Agusta Shugaba Tinubu ya rantsar da ministocin da majalisar dattawa ta tantance tare da amincewa da su
  • Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, yana daga cikin waɗanda a ka rantsar inda ya zama ministan birnin tarayya Abuja
  • Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya taya Wike murna inda ya nuna ƙwarin gwiwarsa cewa zai yi abin da ya dace

Yola, Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya taya tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, murna bisa muƙamin ministan birnin tarayya Abuja da a ka naɗa shi.

Wike yana daga cikin ministoci 45 da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta a babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa, a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Yi Karya Domin Kare Gwamnatin Tinubu Ba" Sabon Minista Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

Gwamna Fintiri ya taya Wike murna
Gwamna Fintiri ya taya Wike murna kan sabon mukamin da ya samu Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Gwamna Fintiri ya aike da saƙon taya murna ga Wike, inda ya bayyana ba shi muƙamin da a ka yi a matsayin wanda ya cancanta.

Ya nuna fatansa kan cewa tarihin kawo cigaba da tsohon gwamnan yake da shi zai amfani birnin tarayya Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin wani rubutu da ya sanya a shafinsa na Twitter, wanda Legit.ng ta ci karo da shi a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, Fintiri ya rubuta cewa:

"Ina taya ka murna kan tsallake tantancewar majalisar dattawa da naɗa ka a matsayin ministan birnin tarayya Abuja.
"Mai girma Ezenwo Nyesom Wike ka kafa tarihi ta hanyar yin shugabanci mai kyau bisa abin da mutane su ke buƙata a lokacin da kake gwamnan jihar Rivers, wanda na yi amanna hakan ne ya sanya ka samu wannna muƙamin.

Kara karanta wannan

Wike Ya Fara Aiki Matsayin Ministan Abuja, Ya Fadi Irin Gine-Ginen Da Zai Rushe

"Na yi amanna cewa za ka cigaba da aiki wajen cigaban birnin tarayya Abuja kamar yadda ka yi a jihar Rivers lokacin kana matsayin gwamna."
Ɗan uwana kuma abokina, ina ƙara taya ka murnar wannan muƙamin da ka samu. Na san cewa ka yi aiki tuƙuru domin kai wa wannan matsayin, na yi murna cewa an lura da nasarorin da ka samu ta hanyar ba ka wannan sabon aikin. Hakan ya cancanta sosai."

Kotu Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar Gwamnan Kano

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano, ta tanadi hukuncinta kan shari'ar gwamnan jihar.

Jam'iyyar APC na neman kotun ta ƙwace nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP, ta ba ɗan takararta Nasiru Yusuf Gawuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng