Benue: Yan Bindiga Sun Harbe Kwamandan Rundunar Tsaro Har Lahira

Benue: Yan Bindiga Sun Harbe Kwamandan Rundunar Tsaro Har Lahira

  • Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kashe kwamandan gunduma na rundunar kula da kiwon dabbobi a jihar Benuwai
  • Rahoto daga bakin waɗanda abun ya faru a idonsu ya nuna cewa kwamandan ya mutu ne bayan maharan sun harbe shi a ƙirji
  • Shugaban rundunar na jiha, Linus Zaki, ya ce wannan ne mutum na huɗu daga cikin jami'ansa da aka kashe a yankin Ukum

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benue state - Wasu miyagun 'yan bindiga sun halaka kwamandan rundunar tsaron dabbobi har lahira a yankin ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benuwai.

Gwamnatin jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya ce ta kafa rundunar domin tabbatar da bin dokar haramta kiwon dabbobi a fili.

Harin yan bindiga a jihar Benuwai.
Benue: Yan Bindiga Sun Harbe Kwamandan Rundunar Tsaro Har Lahira Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa Ganau sun bayyana cewa kisan gillan da aka yi wa kwamandan na gunduma, ya jefa mutane cikin tashin hankali da fargaba.

Kara karanta wannan

Kaico: An kutsa gidan attajiri a Arewa, an sace matarsa mai shayar da jariri

Mutanen yankin sun ce marigayi kwamandan, wanda aka bayyana sunansa da Jarule Likita, shi ke kula da gundumar Mbatian da ke ƙaramar hukumar Ukum kafin kashe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wasu majiyoyi daga yankin, mamacin ya rasa rayuwarsa ne bayan 'yan bindigan sun harbe shi a wurare da dama a ƙirjinsa kuma lamarin ya faru a Tine-Nune, rahoton The Whistler ya tattaro.

Marigayi Likita ya zama mutum 5 daga cikin kwamandojin gunduma da 'yan bindiga suka kashe a yankin ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benuwai a baya-bayan nan.

Mutum 4 kenan aka kashe

A wata hira ta wayar salula, kwamandan rundunar tsaron kiwon dabbobi ta jihar Benuwai, Linus Zaki, ya ce a baya-bayan nan kaɗai an kashe masa jami'ai huɗu a Ukum.

A kalamansa, Zaki ya ce:

"Yanzu nake samun labarin cewa wasu ɗauke da makamai ne suka kai masa hari suka yi ajalinsa (Likita). Shi kaɗai suka kashe yau, kuma ba yanzu suka fara ba, haka su ke kashe mana jami'ai."

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Shugaban Nijar Ya Bude Baki, Ya Fadi Shekarun da Zai Yi kan Mulki

"Mutum uku daga cikin jami'aina sun rasa rayukansu watanni biyu da suka wuce, suna zuwa ne kawai su harbe su sannan su gudu, an faɗa mun cewa ana kiran maharan da 'yan bindigan da ba'a sani ba."
"Akwai wanda daga zuwa ya ɗauko matarsa kawai aka harbe shi har lahira, haka aka yi wa wasu jami'an mu, ban san daga ina maharan suka fito ba."

Zanga-zanga ta ɓarke a Kano

A wani rahoton kun ji cewa Masu zanga-zanga sun yi fatali da umarnin rundunar yan sanda reshen jihar Kano, sun fantsama kan tituna.

Kwamishinan rundunar yan sandan jihar Kano, Mohammed Usain Gumel, ya sanar da haramta duk wani nau'i na zanga-zanga a lungu da saƙo na jihar Kano bayan gano tuggun 'yan siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262