Sojojin Najeriya Sun Kama Surukin Dogo Gide a Kasuwar Kaduna
- Surikin riƙaƙƙen ɗan ta'addan nan Dogo Gide, ya shiga hannu a wani samame da jami'an tsaro suka kai wata kasuwa a jihar Kaduna
- Jami'an sun yi nasarar kama surukin na Dogo Gide mai suna Kenkere tare da haɗin gwiwar 'yan sintiri
- An bayyana cewa Dogo Gide kan fake a gidan surukin na sa domin ƙaddamar da hare-hare a yankin
Kagarko, jihar Kaduna - Jami'an 'yan sanda da haɗin gwiwar 'yan sintiri, sun yi nasarar cafke sirikin riƙaƙƙen ɗan ta'addan nan Dogo Gide da aka bayyana sunansa da Kenkere.
An kama Kenkere ne dai a wata kasuwa da ke Kagarkon jihar Kaduna, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.
Yadda sojoji suka kama surukin Dogo Gide
Wani jami'in tsaro da ya nemi a dakatar sunansa ya bayyana cewa jami'an tsaro sun yi nasarar kama surukin na Dogo Gide a kasuwar Kagarko, ranar Alhamis da ta gabata.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce tuntuni jami'an tsaro ke neman Kenkere, wanda mazaunin wata rugar Fulani ce a ƙauyen Janjala da ke yankin na Kagarko.
Ya kuma bayyana cewa riƙaƙƙen ɗan ta'addan da ya addabi yankin Arewacin Najeriya wato Dogo Gide, yana auren ɗaya daga cikin 'ya'yan Kenkeren.
Dogo Gide na zama a gidan surukin na sa
Jami'in tsaron ya kuma bayyana cewa sun samu bayanai na sirri da ke nuna cewa Dogo Gide ya kan fake a gidan surukin na sa da ke nan Janjala a lokuta da dama.
Ya ƙara da cewa sun kuma samu tabbacin cewa hare-haren da ake kai wa da kuma garkuwa da mutane da ake yi a yankin duk yaran Dogo Gide ne ke yi.
Dogo Gide dai shi ne wanda ake zargin ya kitsa kai harin da 'yan ta'adda suka kai wa jirgin saman sojojin Najeriya a makon da ya gabata.
Harin ya yi sanadin mutuwar sama da sojojin Najeriya 30 kamar yadda gidan talabijin na Channels ya wallafa.
'Yan bindiga sun halaka mutane 5 a jihar Katsina
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani farmakin 'yan bindiga da ya yi sanadin rasa rayukan mutane biyar a ƙaramar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina.
A yayin harin, 'yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutanen da dama da galibinsu mata ne da kuma dabbobi masu tarin yawa.
Asali: Legit.ng