Abdulrasheed Bawa: Femi Falana Ya Bukaci Tinubu Ya Saki Tsohon Shugaban EFCC
- Femi Falana (SAN) ya bukaci gwamnatin tarayya da ta saki dakataccen shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa
- Lauyan mai kare haƙƙin ɗan Adam ya ce yakamata gwamnatin tarayya ta kai Bawa kotu ko ta sake shi idan ba ta da hujja a kansa
- Falana ya bayyana cewa wa'adin umarnin tsare Bawa da kotun majistare ta bayar ya ƙare kuma bai inganta ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Femi Falana (SAN), ya bayyana dalilin da ya sanya gwamnatin tarayya yakamata ta saki dakataccen shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.
Falana ya bayyana cewa yakamata hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta saki Bawa idan har ba ta da hujjar yana da hannu wajen aikata laifuka, cewar rahoton The Nation.
Ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 19 ga watan Agusta 2023 a wata sanarwa mai taken 'A saki Abdulrasheed Bawa daga ɗaurin da a ka yi masa saboda wa'adin umarnin tsare shi ya ƙare'.
Ba majistaren da ke da ikon tsare Bawa har kwana 67
"Ba ni da masaniya kan batun cewa an tsare Bawa ne bisa umarnin wata kotun majistare a birnin tarayya Abuja." A cewarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Yana da kyau a lura cewa wa'adin umarnin ya ƙare, bai halatta ba saboda babu kotun majistare a sashe na 493 da sashe 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya da za ta iya bayar da umarnin tsare wanda a ke zargi da laifi fiye da kwana 67 ba tare da yi masa shari'a ba.".
Dalilin da ya sa yakamata DSS ta saki Bawa
Falana ya yi nuni da cewa an tsare Bawa fiye da kwana 56, wanda shi ne adadin kwanakin da za a iya sakaya wanda ake zargi.
"Tabbas a ƙarƙashin doka adadin kwanaki 56 ne na umarnin sakaya wanda a ke zargi. Saboda haka, tun da ya wuce adadin kwanakin da kundin tsarin mulki ya tanada, yakamata a umarci DSS ta saki Abdulrasheed Bawa daga haramtaccen ɗaurin da ta yi masa ba tare da ɓata lokaci ba.” A cewarsa.
An Bankado Tuggun Da a Ke Yi Wa Atiku
A wani labarin kuma, wata ƙungiya mai zaman kanta ta bankaɗo wani sabon tuggu da a ke shiryawa kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Ƙungiyar Facd Of Waziri-Nigeria (FOWN), ta zargi Shugaba Tinubu da kitsa yadda za a ɓata sunan Atiku Abubakar.
Asali: Legit.ng