'Yan Bindiga Sun Sace Wata Mata Mai Shayarwa ’Yar Shekara 20 da Wasu 3 a Bauchi

'Yan Bindiga Sun Sace Wata Mata Mai Shayarwa ’Yar Shekara 20 da Wasu 3 a Bauchi

  • An ruwaito yadda wasu tsagerun ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wata mata mai shayarwa a wani yankin jihar Bauchi
  • An kutsa gidan wani Alhaji tare da sace matarsa mai shekaru 20, an kum sace wasu mutanen daban a farmakin
  • Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fama da farmakin ‘yan bindiga da kuma kisa ba gaira babu dalili a yankin

Jihar Bauchi - Wasu ‘yan bindiga da ke addabar mazauna karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi sun sake farfadowa tare da kai farmaki kan wasu al’ummomi uku a yankin inda aka yi garkuwa da mutane 4, Tribune Online ta ruwaito.

Idan dai baku manta ba, rundunar ‘yan sandan jihar tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro sun kai farmaki dazuzzukan Burra da Yadagungume inda suka yi nasarar kashe wasu ‘yan bindigar tare da cafke wasu a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

100 sun mutu: Yanzu haka 'yan Boko Haram da ISWAP suna can suna ta kwabza yaki a Borno

Wata majiya mai tushe ta shaida cewa, a daren ranar Alhamis ne ‘yan ta’addan suka kai hari a unguwar Sanger da ke kauyen Kwangoro inda suka yi awon gaba da mutum guda.

Yadda masu garkuwa da mutane suka sace mata mai shekaru 20 a Bauchi
An sace amaryar Alhaji a jihar Bauchi | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Nawa ake bukata kudin fansa?

Sai dai, majiyar ta ce ba za iya tantance ko nawa suke bukata ba a matsayin fansan da suke nema na garkuwar da suka yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyar ta kara da cewa, a ranar Asabar da daddare ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Billiri Gorore da ke cikin yankin Lumbu inda suka yi garkuwa da mutane biyu wato; Alhaji Chibi da Alhaji Siba.

An tattaro cewa ‘yan bindigan a wani samame na daban, sun kai hari garin Yadagungume a daren ranar Asabar, inda suka yi awon gaba da wata mata mai shayarwa, matar daya daga cikin ‘yan kasuwar da ke garin, wadda ya kubuta daga farmakin.

Kara karanta wannan

Kaduna: Matan Aure Sunyi Zanga-Zanga Kan Yunwa Da Tsadar Abinci, Sun Roki Tinubu Ya Kawo Sauyi

Yadda aka kutsa gidan Alhaji

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na safe, inda ‘yan bindigar suka shiga gidan wani Alh Abdussalam Jibrin Yaudo da karfi a unguwar Yadagungume.

A nan ne suka sace matarsa mai shayarwa mai suna Adama Abdussalam mai shekaru 20 kacal a duniya, kafar labarai ta Linda Ikeji ta tattaro.

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da bincike kan lamarin da kuma kokarin tabbatar da an kubutar da wadanda aka sacen.

‘Yan bindiga sun sace matar faso

‘Yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun sace matar wani faston cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) a jihar Kwara.

Ƴan bindigan wadanda sun kai su mutum bakwai, sun sace matar faston ne a kauyen Elerinjare da ke ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

DSS: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Shirin Kai wa Mutane Mugun Hari a Jirgin Abuja-Kaduna

Matar faston mai suna Mrs Blessing Ajiboye, an sace ta ne tare da masu taimaka mata su biyu a shagonta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.