Kungiyar FOWN Ta Zargi Tinubu Da Kokarin Bata Sunan Atiku Abubakar

Kungiyar FOWN Ta Zargi Tinubu Da Kokarin Bata Sunan Atiku Abubakar

  • Ƙungiyar Face Of Waziri-Nigeria (FOWN) na zargin cewa Shugaba Tinubu na son ganin ya ɓata sunan Atiku Abubakar
  • Ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa shugaban ƙasar yana son ɓata sunan Atiku ne saboda ƙarar da ya shigar da shi a Amurka kan takardun karatunsa
  • Ƙungiyar ta yi nuni da cewa ana son a dusashe tauraruwar Atiku Abubakar musamman a yankin Arewacin Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna Face Of Waziri-Nigeria (FOWN), ta zargi Shugaba Tinubu da ƙoƙarin ɓata sunan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a idon magoya bayansa.

Ƙungiyar ta yi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ƙarshen mako, wacce Darekta Janar ɗin ta, Mr Bukky Adeniyi ya rattɓawa hannu, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Abdourahmane Tchiani Ya Fadi Matakin Da Za Su Dauka Idan ECOWAS Ta Kawowa Nijar Hari

An zargi Tinubu da kokarin bata sunan Atiku
Bola Tinubu tare da Atiku
Asali: Facebook

Ƙungiyar a cikin sanarwar ta yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta fusata kan ƙoƙarin da Atiku Abuabakar yake yi wajen ganin ya gano takardun karatun Tinubu, ta hanyar ƙarar da shigar a ƙasar Amurka.

A cewar FOWN, Tinubu ba zai saurara ba har sai ya ga ya goge duk wasu laifuka da ya yi a baya, musamman da a yanzu ya ga sun zo sun zama masa ƙarfen ƙafa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu na shirya sabon tuggu, cewae FOWN

FOWN ta yi nuni da cewa akwai tuggun da ake shiryawa domin ɓata sunan Atiku, da rage masa farin jini a Arewacin Najeriya, ta hanyar yaɗa ƙarairayi a kansa.

"Hanyar da aka bi domin cimma wannan mummunan aikin ta haɗa da yin amfani da kafafen sadarwa, malaman addini a Arewacin Najeriya, da amfani da Shariff Nastura, shugaban gamayyar ƙungiyoyin Arewa, domin kawo ruɗani a cikin jam'iyyar PDP." A cewar FOWN.

Kara karanta wannan

Janar Tchiani Ya Yi Kaca-Kaca Da ECOWAS, Ya Bayyana Matakin Dauka Na Gaba

Ƙungiyar ta yi zargin cewa tsohon gwamna Nyesom Wike da magajinsa a jihar Rivers, Siminalayi Fubara, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da wasu gwamnonin PDP da ke tare da su, an ba du maƙudan kuɗaɗe domin tabbatar da kawo ruɗani a jam'iyyar PDP..

Ministocin Tinubu Masu Karbar Fansho

Kuna da labari cewa akwai wasu daga cikin ministocin shugaban ƙasa Bola Tinubu da a kd biya kuɗaɗen fansho daga asusun jihohinsu.

Ministocin dai tsofaffin gwamnoni waɗanda suka yi mulki a jihohinsu kafin Tinubu ya ba su muƙamin minista a gwamnatinsa.

Wike, Matawalle da Badaru na daga cikin ministocin da ke karɓar fansho daga asusun jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng