Buhari Ya Mika Sakon Ta'aziyya Ga Tinubu Da Iyalan Sojojin Da Su Ka Mutu A Harin Neja

Buhari Ya Mika Sakon Ta'aziyya Ga Tinubu Da Iyalan Sojojin Da Su Ka Mutu A Harin Neja

  • Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasar Najeriya ya jajantawa iyalan sojojin da su ka mutu a jihar Neja
  • Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya fitar a yau Asabar 19 ga watan Agusta
  • Buhari ya jajantawa iyalan wadanda su ka rasu tare da mika sakon ta'aziyya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa kan kisan sojoji a jihar Neja da kuma faduwar jirgin sojoji a jihar.

Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya fitar a yau Asabar 19 ga watan Agusta, Tribune ta tattaro.

Buhari ya mika sakon ta'aziya ga Tinubu kan mutuwar sojoji a jihar Niger
Buhari Ya Yi Martani Kan Mutuwar Sojoji A Jihar Neja. Hoto: Muhammadu Buhari, Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Meye Buhari ya ce ga Tinubu?

Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, cewar gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

A'a ba laifinmu ba ne: Sanata Ya Fadi Wadanda Su Ka Hana El-Rufai Zama Minista

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojoji 36 da aka kashe da kuma wadanda su ka mutu bayan jirgin sojojin ya yi hatsari.

Buhari a cikin sanarwar ya ce:

"Na kadu da samun labarin mutuwar sojojin mu da aka musu kwantan bauna da kuma faduwar jirgin sojoji.
"Ina mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda su ka mutu, ina addu'ar Allah ya ba wa wadanda su ka ji ciwo lafiya da gaggawa."

Buhari ya kuma mika sakon ta'aziyya ga shugaban kasa, Bola Tinubu kan babbar rashi da aka yi a kasar.

Sakon Buhari ga Tinubu da sojoji

Punch ta tattaro Buhari na cewa:

"Ina mika sakon jaje ga shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu da kuma iyalan mamatan.
"Yadda sojojin mu ke da jajircewa a aiki, ina da tabbacin za su shawo kan wannan matsalar."

Kara karanta wannan

Wahalar da Ake Sha Tamkar Nakuda ce, Bola Tinubu Ya Ce Za a Haifi Jariri

Rundunar Tsaro Ta Bayyana Adadin Sojojin Da Aka Kashe A Neja

A wani labarin, rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta 36 yayin da 'yan bindiga su ka yi musu kwanton bauna a jihar Neja.

Kakakin rundunar, Edward Buba shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai inda ya bayyana adadin sojojin da aka kashe a ranar 14 ga watan Agusta.

Wannan na zuwa ne bayan sojojin sun kara kaimi don kakkabe 'yan bindiga da su ka addabi jihar a kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.