Buhari Ya Jinjinawa Janar Ibrahim Babangida, Shekaru 38 Da Masa Juyin-Mulki
- Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi na musamman a game da Ibrahim Badamasi Babangida
- Tsohon shugaban kasar ya ce IBB kamar yadda akafi sanin shi, ya na burin cigaban Abuja da Najeriya
- Buhari ya yi magana ne ta bakin Garba Shehu daidai lokacin da Babangida ya cika shekaru 82 a Duniya
Abuja - Tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya dauki lokaci ya taya Ibrahim Badamasi Babangida murnar kara shekara a Duniya.
Mai girma Muhammadu Buhari ya shga cikin jerin masu farin ciki da cikar Ibrahim Badamasi Babangida shekarara 82 ya a kan ban kasa.
Buhari ya aika da sakon taya murnarsa ne ta bakin Mai magana da yawunsa, Garba Shehu a jiya.
Malam Garba Shehu a jawabin da ya fitar a shafinsa na Twitter, ya ce Muhammadu Buhari ya bayyana magajinsa da fitaccen jami’in soja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Baya ga yabo da ya kwararawa Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, Buhari ya yi addu’a ga Ubangiji ya karawa tsohon lafiya.
IBB: Jawabin Malam Garba Shehu
FITACCEN JAMI’I, TSOHON SHUGABAN KASA YA YABI IBB YAYIN DA Y CIKA 82.
A lokacin cikarsa shekara 82, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiko da fatan alheri ga tsohon shugaban mulkin soka, Ibrahim Babangida.
Ya yaba masa a matsayin fitaccen jami’i wanda yake da burin cigaban babban birnin tarayya Abuja da kasar nan.
Tsohon shugaban kasar ya yi wa Janar Babangida fatan tsawon rai da karin lafiya.
- Garba Shehu
Atiku da Kwankwaso sun aikawa Babangida sako
Tsohon Gwamna kuma tsohon Ministan tsaro, Rabiu Kwankwaso ya yi amfani da shafin Twitter, ya taya IBB murnar zagayowar ranarsa.
Tribune ta ce Atiku Abukar kuwa ya aika tawaga ne a karkashin jagorancin Muazu Babangida Aliyu, su ka kai wa Babangida wasikarsa.
Mr. Paul Ibe ya ce ‘yan tawagar ta kunshi shi karon kan shi; Ibrahim Maisule, Hon. Abdullahi Hussaini MaiBasira da Mohammed Atiku.
Rikicin Najeriya v Nijar
An ji labari Farfesa Salisu Shehu ya gargadi Bola Tinubu kan yakar Nijar, fitaccen malamin addinin musulunci, Kabir Gombe ya shaida haka.
Sakataren na kungiyar Izala na Najeriya (JIBWIS), Kabiru Gombe ya ce sun yi wa shugaban Najeriya gamsasshen jawabi kafin su shiga Nijar.
Asali: Legit.ng