'APC Karkashin Ganduje Na Iya Mulkar Najeriya Fiye Da Shekaru 60', Zailani
- Tsohon kakakin majalisar jihar Kaduna, Ibrahim Zailani ya ba da tabbacin cewa jam'iyyar APC za ta yi mulki har shekaru 60
- Zailani ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar tsoffin 'yan majalisar wakilai ta Tarayya zuwa ofishin Ganduje
- Ya bayyana cewa APC a karkashin jagorancin Ganduje za ta yi abin da ba a ta ba yi ba a mulkin kasar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Tsohon kakakin majalisar jihar Kaduna, Yusuf Ibrahim Zailani ya ce jam'iyyar APC za ta iya mulki har na tsawon shekaru 60.
Zailani ya ce yadda shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya dauko hanya hakan zai matukar ba wa jam'iyyar tsawon rai a kasar.
Meye Zailani ya ce kan Ganduje da APC?
Tsohon kakakin ya bayyana haka ne a yau Alhamis 17 ga watan Agusta a Abuja yayin ziyarar goyon baya ga Ganduje, Ripples Nigeria ta tattaro.
Cin Hanci: Abba Gida Gida Ya Tsorata, Ya Bukaci Binciken Gaggawa A Kotun Sauraran Korafe-Korafen Zabe
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zailani ya jagoranci tsoffin 'yan majalisar wakilai ta Tarayya zuwa ofishin shugaban jam'iyyar da ke Abuja.
Ya ce tabbas a wannan lokaci da jam'iyyar ke hannun Ganduje, APC za ta Yi abin da ba a taba yi ba na daukar lokaci ta na mulki, cewar Punch.
Ganduje zai ja ragamar APC su yi mulki har shekaru 60
A cewarsa:
"Muna da tabbacin cewa a kanka na gudanar da tafiyar wannan jam'iyyar a Najeriya har na tsawon shekaru 60.
"Muna da tabbacin za ka iya, tabbas za ka iya saboda muna da kwarin gwiwa a kanka.
"A nan wurin, muna wakiltar kasa baki daya ne tunda ko wane yanki na kasar ya samu wakili.
"A yanzu ba ma majalisa, amma kuma muna jin jam'iyyar a zuciya kuma muna shirye don gabatar da duk wani aiki a jam'iyyar.
Shari'ar Gwamnan Kano: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Roki Yan Najeriya Su Taya APC Addu'ar Samun Nasara Kan PDP
Yayin martanin shi, Abdullahi Ganduje ya godewa tawagar bisa wannan ziyara, tare da kwabarsu da su rika sauke nauyin da ke kan su na jama'a, Naija News ta tattaro.
An Nada Ganduje Shugaban Jam'iyyar APC
A wani labarin, an zabi Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyar APC mai mulki a Abuja.
An nada Ganduje ne a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da ya samu halartar Shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng