Sarkin Musulmi Ya Ce Tabarbarewar Tsaro Ke Hana Yi Wa Yara Rigakafi A Arewa

Sarkin Musulmi Ya Ce Tabarbarewar Tsaro Ke Hana Yi Wa Yara Rigakafi A Arewa

  • Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad ya bayyana dalilin da yasa yara a Arewacin Najeriya ke rasa samun cikakken rigakafi
  • Ya ce babban abin da ya jawo wannan matsalar ita ce rashin tsaro musamman a jihohin Kaduna da Niger da Katsina
  • Ya roki sauran sarakunan gargajiya da su ci gaba da ba da hadin kai wurin tabbatar da cewa yaran Arewacin Najeriya sun samu rigakafi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad ya koka kan yadda rashin tsaro da sauran matsaloli ke hana yaran Arewacin Najeriya samun rigakafi.

Sultan ya bayyana haka ne yayin ganawa da sarakunan gargajiya a Kaduna don neman mafita a kan matsalar.

Sarkin ya fadi abin da ke hana rigakafi a Arewacin Najeriya
Sarkin Musulmi Ya Bayyana Matsalar Rashin Tsaro A Matsayin Cikas Ga Rigakafin Yara A Arewa. Hoto: Daily Post.
Asali: UGC

Wa su ka halarci taron tare da Sarkin Musulmi?

Ganawar wanda Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko (NPHCDA) ta shirya da hadakar Gidauniyar Sultan na zaman lafiya da ci gaba, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ganawar, an tattauna batutuwa da dama da su ke hana yara a Arewacin Najeriya samun rigakafi kamar sauran yara a fadin kasar.

Wadanda su ka samu halartar bikin sun hada da Hukumar UNICEF da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da kuma mataimayar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe.

Me ye Sarkin Musulmi ya ce?

Sultan ya ce:

"Makasudin wannan ganawar ita ce samar da mafita ga yara musamman daga jihohin Niger da Kaduna da kuma Katsina don samun rigakafi.
"Wannan shi ne babban aikin mu a matsayin mu na sarakunan gargajiya a kasar.
"Ba mun rasa goyon baya ba ne daga mutanen mu, abin da muka rasa shi ne aiwatar da abu, wannan dalilin ya sa aka bar mu a baya a harkar rigakafi."

A martaninshi, babban daraktan hukumar, Faisal Shuaib ya godewa sarakunan gargajiya a kan irin gudummawar da su ke bayarwa a harkar rigakafin, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: An Fadawa Tinubu Abu Daya Tak Da Zai Yi Don Shawo Kan Matsalar Tsaro A Jihar Arewa, Ta Nemi Bukata

Ya ce karfin mulkinsu na da matukar tasiri wurin samar da lafiyayyar al'umma, ya roke su da su ci gaba da ba da gudunmawa don samun nasara.

Sarkin Musulmi Ya Yi Allah Wadai Da Kona Qur'ani A Sweden

A wani labarin, sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad ya soki gwamnatin kasar Sweden kan kona Qur'ani da aka yi a kasar.

Sultan ya ce wannan cin zarafi ne da kuma neman tsokana inda ya bukaci da a dauki matakin gaggawa a kan haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.