Godwin Emefiele Ya Gurfana a Gaban Kuliya Domin Amsa Zarge-zargen Da Ake Yi Ma Sa

Godwin Emefiele Ya Gurfana a Gaban Kuliya Domin Amsa Zarge-zargen Da Ake Yi Ma Sa

  • A ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta ne tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya gurfana a gaban kotu
  • Ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya ne ya shigar da gwamnan wato Emefiele bisa tuhumar badaƙalar kuɗaɗe
  • Ana sa ran za a yankewa Godwin Emefiele hukunci kan badaƙakar kuɗaɗen da suka kai naira biliyan 6.9

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - An bayyana cewa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, ya gurfana a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maitama Abuja.

Ana zargin Emefiele da badaƙalar maƙudan kuɗaɗe da suka kai naira biliyan shida da digo tara a lokacin da yake gwamnan babban banki.

Mai shari'a Hamza Muazu ne zai jagoranci yanke hukunci kan tsohon gwamnan babban bankin a yau Alhamis, 17 ga watan Agusta kamar yadda The Cable ta wallafa.

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Matashi Gaban Kuliya Bisa Zargin Tafka Ta'asa a Makabarta a Legas

Godwin Emefiele ya gurfana a gaban kotu
Godwin Emefiele ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya. Hoto: DSS
Asali: Twitter

A kan menene Emefiele ya gurfana a kotu

Emefiele ya gurfana ne a gaban kotun bisa tuhume-tuhume guda 20 da Gwamnatin Tarayya ta shigar a kansa da suka shafi badaƙalar maƙudan kuɗaɗe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin Emefiele da haɗa baki da wata abokiyar aikinsa Sa'adatu Yaro da kamfaninta mai suna April1616 Investment Limited wajen karkatar da kuɗaɗen da suka kai naira biliyan 6.9 da ake tuhumarsu da tattarewa.

Tun bayan dakatar da shi da Shugaba Tinubu ya yi daga shugabancin babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya kasance a tsare a hannun jami'an hukumar DSS.

An dage sauraron ƙarar ta Emefiele

Sai dai ba a samu damar yanke hukunci a zaman kotun da ya gudana yau ba sakamakon rashin zuwan matar da ake tuhumar Emefiele a tare da ita gaban kotun kamar yadda aka wallafa a shafin yanar gizo na Channels TV.

Kara karanta wannan

Masanin Tattalin Arziƙi Ya Fadi Abinda Zai Faru Idan Ministocin Tinubu Suka Fara Aiki

Biyo bayan hakan ne mai shari'a Hamza Muazu ya sanar da ɗage sauraron ƙarar da kuma yanke hukunci zuwa ranar Laraba, 23 ga watan Agustan da muke ciki.

An bayyana cewa lauyoyin Godwin Emefiele, sun yi ƙoƙarin hana 'yan jarida da sauran mutane ɗaukar hotunansa a yayin da shi kuma yake ci gaba da amsa kiran waya.

FG za ta janye tuhumar mallakar makamai kan Emefiele

Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan yunƙurin da Gwamnatin Tarayya na ganin ta janye tuhumar da take yi wa dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya kan mallakar makamai.

A ranar Talata da ta gabata ne, lauyoyin Gwamnatin Tarayya suka shigar da buƙatar janye tuhumar mallakar makamai da take yi wa Emefiele a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng