Mayakan Boko Haram 82 Sun Halaka a Wani Rikicin Kabilanci a Jihar Borno
- Mayaƙan Boko Haram masu yawan gaske sun sheƙa zuwa barzahu bayan rikicin ƙabilanci ya ɓarke a tsakaninsu a jihar Borno
- Aƙalla sama da mayaƙa 82 ne suka gamu da ajalinsu a rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙabilun Hausa, Fulani, Kanuri da Buduma
- Rikicin dai babban koma baya ne ga mayaƙan waɗanda su ke shan ragargaza a wajen dakarun sojojin Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Borno - Aƙalla ƴan ta'addan Boko Haram 82 ne suka baƙunci lahira a wani rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a tsakanin mayaƙan ƙungiyar.
Lamarin ya auku ne a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno. Majiyoyi a Baga da yankunan da ke a tafkin Chadi sun tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Daily Trust a ranar Laraba.
Yadda rikicin ya auku
Wani daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa rikicin ya ɓarke ne bayan an halaka mayaƙan ƙungiyar ƴan ƙabilar Buduma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa kwamandan ƙungiyar a tsibirin Bukkwaram, shi ne ya halaka su bayan sun yi ƙoƙarin miƙa wuya ga dakarun sojoji a ranar Talata.
Takwarorinsu da suka gayawa shirin su na miƙa wuya ne suka ci amanar su, suka gayawa kwamandan shirin su na miƙa wuya. Daga baya an tare su sannan aka kai su tsibirin Bukkwaram, inda kwamandan ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar harbi.
"Bayan an halaka su, sai rikicin ƙabilanci ya ɓarke a tsakanin ƙabilu huɗu na mayaƙan, Hausa, Fulani, Kanuri, da Buduma." A cewar majiyar.
"Wasu daga cikin mayaƙan ƴan ƙabilar Buduma sun zargi kwamandan da tsaurarawa duba da yadda su ke asarar mayaƙa a yankin cikin ƴan kwanakin nan."
Ya bayyana cewa hakan ya sanya aka kira taro inda duka kwamandojin suka cimma yarjejeniyar cewa mayaƙan za su iya barin wajen su koma inda su ke so.
Harin 'Yan Bindiga: Gwamnan Jihar Neja Ya Sanya Labule Da Shugaban Hukumar Sojojin Saman Najeriya, Bayanai Sun Fito
Wani kwamanda ya kawo tirjiya
Sai dai, wani daga cikin kwamandojin, Baduma Bakura, ɗan ƙabilar Buduma, wanda ya zo taron daga sansanin Ali Mandula a Jamhuriyar Nijar, ya ƙi yarda da matsayar da aka cimma.
Majiyar ya cigaba da cewa:
"Ya ce ya zo ne domin ya yi bincike kan kashe masa ƴan uwa da aka yi inda ya yi barazanar harbin duk wanda ya yi ƙoƙarin barin wajen taron, amma ana cikin cacar bakin sai wani daga cikin mayaƙan ɗan ƙabilar Fulani ya harbe Baduma har lahira."
"Musayar wutar da ta biyo bayan hakan ta sanya mayaƙa 82 sun sheƙe barzahu. Babu wanda zai ce ga mayaƙan Boko Haram ko ISWAP a cikinsu. Faɗan ƙabilanci ne kawai."
Boko Haram Ta Cafke Mayakan ISWAP
A wani labarin kuma, ƙungiyar Boko Haram ta cafke mayaƙan ƙungiyar ISWAP 57 a wani farmaki a jihar Borno.
Daga cikin mayaƙan da aka cafke har da kwamandojin ƙungiyar guda uku, inda aka kulle su a matsayin fursunonin yaƙi.
Asali: Legit.ng