ECOWAS Ta Buƙaci Sojojin Nijar Su Mika Mulki, Su Koma Su Ci Gaba Da Tsaron Ƙasarsu
- Wasu 'yan ta'adda ɗauke da muggan makamai sun halaka sojojin Nijar a wani hari da suka kai mu su
- Kungiyar ECOWAS ta nuna rashin jin dadinta bisa faruwar wannan mummunan lamari
- Sai dai ECOWAS ta yi kira ga sojojin da su mayar da mulki hannun Mohamed Bazoum domin su mayar da hankali kan tsaron ƙasa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), ta yi martani dangane da kashe sojojin jamhuriyar Nijar da wasu 'yan ta'adda suka yi.
A wani saƙo da aka wallafa a shafin ECOWAS na Twitter, ƙungiyar ta yi Allah wadai da harin da 'yan ta'addan suka kai a kan sojojin na Nijar.
ECOWAS ta buƙaci sojojin Nijar su mayarwa Bazoum mulki
Bayan Allah wadai da harin 'yan ta'addan kan sojojin jamhuriyar Nijar da ECOWAS ta yi, ta nemi sojojin su yi babban abinda ya dace.
Shugabannnin Rundunonin ECOWAS Za Su Yi Taro Dangane Da Umarnin Ɗamarar Yaƙi Da Sojojin Nijar Da Aka Ba Su
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
ECOWAS ta nemi sojojin su mayar da mulki hannun hamɓararren shugaban ƙasar ta Nijar Mohamed Bazoum da suka yi wa juyin mulki a baya.
ECOWAS ta kuma shawarci sojojin su koma bakin daga domin tsare ƙasar daga hare-haren 'yan ta'adda bayan mayar da mulkin hannun farar hula.
Fargabar yaƙi yayin da hafsoshin tsaron ECOWAS ke shirin yin taro
A baya Legit.ng ta yi rahoto kan taron da shugabannin rundunonin tsaron ƙasashen ECOWAS ke shirin yi a makon nan da muke ciki.
Shugabannin rundunonin tsaron na ECOWAS sun tsaida ranar Alhamis, 17 ga watan Agustan da muke ciki a matsayin ranar da za su taru domin tattauna yiwuwar amfani da ƙarfin soji kan jamhuriyar Nijar.
An bayyana cewa shugabannin tsaron ƙasashen ECOWAS 11 ne za su halarci taron da za a yi a Accra babban birnin ƙasar Ghana.
An samu rabuwar kai a majalisar ECOWAS
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan rarrabuwar kawunan da aka samu tsakanin 'yan majalisun ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) kan tura sojoji Nijar.
Wasu daga cikin 'yan majalisar ta ECOWAS sun amince da tura dakaru domin su karɓi mulki ta ƙarfi, a yayinda wasu kuma suka nuna ƙin amincewarsu.
Asali: Legit.ng