Ganganci Ne: Yadda Malamar Makaranta Ta Sharbawa Daliba Zane 4 a Fuska
- Wata uwa ta wallafa wani hoto da ke nuna yadda malamar makaranta ta sharbawa diyarta zane har hudu a fuska
- Hoton zanen guda hudu, wanda ya yi kama da billen wata kabila ya haifar da cece-kuce bayan an wallafa shi a Facebook
- Malamar makarantar ta fada ma mahaifiyar cewa kuskure ne, amma mutane sun ce da gangan ta aikata haka
Wata uwa ta ce wata malamar makaranta ta sharbawa diyarta zane guda hudu a fuska ba tare da izini ba.
Wani hoton yarinyar da shafin gidan radiyon Ilorin, Sobi Fm, ya wallafa a Facebook ya nuno yarinyar dauke da zane hudu a gefen kuncinta na dama.
Amma dai malamar ta yi ikirarin cewa akasi aka samu, cewa ba da gangan ta aikata hakan ba.
Malamar ta ce tana girki ne kuma ba ta san cewar yarinyar na tsaye a gefenta ba. Wani cokali mai yatsu da ya dauki zafi da take rike da shi a hannu shine ya taba kuncin yarinyar bisa kuskure.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Malamar makaranta ta yi wa yarinya zane hudu bisa kuskure
Mahaifiyar yarinyar ta kai lamarin dandalin Facebook inda ta tambayi iyaye mata yan uwanta kan abun da za ta yi domin zanen ya bace.
Mahaifiyar yarinyar ta rubuta:
"Iyaye mata a gidan nan don Allah ku taimaki wata uwa mai cike da damuwa, na yi wa diyata rijista a wani makarantar raino da ke kusa da shagona. Don haka bayan tashi, na je don na dauki diyata. Da isa ta wajen, malamarta sai ta fara bani hakuri cewa ta konawa yarinyata fuska bisa kuskure da cokali mai yatsu mai zafi. A cewarta, ta ce bata san yarinyata na tsaye a bayanta ba yayin da take girki. Don haka ga fuskar diyata bayan bakin da ke sama ya daye. Shin zanen zai tafi? Me zan sa don zanen nan ya tafi don Allah?"
Budurwa Ta Hakura Da Biliyan 300 Da Za Ta Gada Don Auren Masoyinta Bakin Fata, Iyayenta Sun Yafewa Duniya Ita
Wasu masu amfani da Facebook sun caccaki malamar makarantar cewa da gangan ta sharbawa yarinyar zanen.
Jama'a sun yi martani
Horllarmilekan Haremu ta ce:
"Zanen nan zai tafi ta hanyar shafa zuma a wajen ciwon, tunda ba wai billen kabila bane da aka yi ya shiga ciki."
Akinsuroju Tolulope ta yi martani:
"Wacce irin makaranta ce wannan? Da gangan ta yi."
Kwara Son ya ce:
"A bari matar ta yi a dayan gefen ma. Kada al'adunmu su bace."
Bayan shekaru 27, matashi na neman mahaifinsa dan Najeriya a Burtaniya
A wani labari na daban, mun ji cewa wani dan Najeriya, wanda baya so a bayyana sunansa, na ci gaba da neman mahaifinsa dan Najeriya bayan shekaru 27 da haihuwarsa a kasar Burtaniya.
Lauyan Najeriya, Abdulmalik A Othman, wanda ya bayyana neman da matashin ke yi a Facebook, ya saki hotunan takardar haihuwar mahaifin nasa da kuma hoton auren iyayen.
Asali: Legit.ng