Musulmai Sun Durfafi Majalisar Jihar Legas Don Nuna Bacin Ransu Kan Nuna Wariya A Mukamai
- Musulmai a jihar Legas sun yi zanga-zangar kin amincewa da sunayen kwamishinoni da Gwamna Sanwo-Olu ya sake
- Musulmin sun koka kan yadda sunayen ke cike da rashin adalci ganin cewa kowa na da hakki a cikin nade-naden gwamnati
- Sun bayyana bacin ransu inda jerin sunayen ke dauke da Musulmai takwas kacal idan akwa kwatanta da na Kiristoci 31
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Legas – Kungiyar Musulmi a jihar Legas ta yi zanga-zanga a bakin majalisar dokokin jihar kan sunayen kwamishinoni da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sake.
Kungiyar ta durfafi harabar majalisar ne a yau Laraba bayan nuna rashin jin dadinsu a sunayen da ke dauke da Musulmai takwas kacal da Kiristoci 31.
Meye al'ummar Musulmai ke cewa?
Ta ce hakan tsantsan rashin adalci ne ga al’ummar Musulmin jihar inda su ka bukaci a yi gyara cikin gaggawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Har ila yau, gwamnatin jihar ta yi fatali da korafin nasu yayin da ta fara tantance kwamishinonin a ranar Litinin 14 ga watan Agusta, cewar Daily Trust.
A yau Laraba 16 ga watan Agusta, al'ummar Musulmai sun durfafi majalisar karkashin jagorancin shugabansu Farfesa Tajudden Gbadamosi.
Gbadamosi ya gabatar da jawabi inda ya ce hakan nuna wariya ne ga al'ummar Musulmai a jihar, Tribune ta tattaro.
Shugabannin kungiyoyin addinin Musulunci da dama sun halarci zanga-zangar inda Farfesa Gbadamosi ya kalubalanci kakakin majalisar, Mudashiru Obasa.
A cikin sanarwar da ya karanta, Farfesa Gbadamosi ya ce al'ummar Musulmai sun yi Allah wadai da rashin adalci da wannan gwamnati ke musu musamman a sunayen kwamishinoni da aka sake.
Me sanarwar Musulman ke dauke da shi?
Sanarwar ta ce:
"Wannan nuna wariya ne da rashin adalci, ta yaya za a ce jerin sunayen kwamishinoni 39 amma Musulmai takwas ne kacal a ciki.
Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati
"Wannan ba sabon abu ba ne a gwamnatin Sanwo-Olu saboda tun farkon hawan shi mulki ya ke nuna wariya ga al'ummar Musulmai a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Misali a 2019, Sanwo-Olu ya nada masu ba shi shawara na musamman 14, guda daya ne kawai Musulmi a ciki.
"Haka ma kwamishinonisa 43 dukkansu Kiristoci ne guda 14 ne kawai Musulmai."
Musulmai Sun Soki Sanwo-Olu Kan Nuna Wariya A Mukamai
A wani labarin, kungiyar malaman addinin Musulunci a jihar Legas ta caccaki Gwamna Sanwo-Olu Babajide kan jerin sunayen kwamishinoni a jihar.
Malaman su ka ce sunayen na dauke da tsantsan rashin adalci da ke da Musulmai takwas kacal a cikin 39.
Asali: Legit.ng