Yaran Dogo Gide Sun Dauki Alhakin Harbo Jirgin Saman Sojin Najeriya Da Ya Yi Hatsari a Neja
- Yaran riƙaƙƙen ɗan ta'addan nan Dogo Gide, sun yi iƙirarin harbo jirgin sojin saman Najeriya
- A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne wani jirgin saman sojojin Najeriya ya yi haɗari a jihar Neja
- Sai dai rundunar sojin saman ta alaƙanta haɗarin jirgin da rashin ingantaccen yanayi da aka samu a lokacin
Neja - Yaran riƙaƙƙen ɗan ta'addan nan da ya ƙware a kai hare-hare da garkuwa da mutane mai suna Dogo Gide, sun yi iƙirarin cewa sune suka harbo jirgin sojin saman Najeriya da ya yi haɗari ranar Litinin ɗin da ta gabata.
A cikin wani ɗan gajeren bidiyo da ya yaɗu a shafukan kafafen sada zumunta, an ga 'yan ta'addan, waɗanda suka ce su yaran Dogo Gide ne, suna bayyana cewa su ne suka harbo jirgin.
Yadda yaran Dogo Gide suka harbo jirgin
A cikin bidiyon da ba tsayi ne da shi ba, an jiyo wata murya na cewa su ne suka harbo jirgin sojojin saman a yayin da ya zo wucewa ta inda suke a Chukuba da ke ƙaramar hukumar Shiroro jihar Neja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya yi iƙirarin cewa sun buɗewa jirgin sojin wuta da bindigunsu ƙirar AK-47 ba tare da tsayawa ba har sai da suka ga ya faɗo ƙasa.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa, ta yi amfani da na'urori domin duba sahihanci bidiyon waɗanda suka nuna ma ta cewa bidiyon sabo ne ba tsoho ba.
Rashin yanayi mai kyau ya janyo haɗarin jirgin
Babban hafsan sojojin saman Najeriya Hassan Abubakar, ya yi ƙarin haske dangane da haɗarin jirgin, inda ya alaƙanta hakan da rashin ingantaccen yanayi.
Harin 'Yan Bindiga: Gwamnan Jihar Neja Ya Sanya Labule Da Shugaban Hukumar Sojojin Saman Najeriya, Bayanai Sun Fito
Ya bayyana hakan ne a lokacin da gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya kai ma sa ziyara a ofishinsa da ke Abuja domin ya jajanta ma sa bisa sojojin da suka rasa rayukansu a haɗarin.
Ya ƙara da cewa suna iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an rage samun faruwar irin wannan mummunan lamarin a yayin da suke gudanar da ayyukansu.
Ya kuma bai wa 'yan Najeriya tabbacin cewa jami'ansu za su ci gaba da bin 'yan ta'adda suna ragargazarsu a duk inda suke.
'Yan ta'adda sun halaka sojoji da dama a Neja
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton sojojin Najeriya sama da guda 20 da 'yan ta'adda suka halaka a jihar Neja.
An bayyana cewa sojojin sun yi yunƙurin tare 'yan ta'addan ne a yayin da suke ƙoƙarin wucewa da shanu da suka sato a wasu ƙauyuka da ke jihar.
Asali: Legit.ng