Shugaban Sojin Sama Ya Bayyana Dalilan Da ke Haddasa Hatsarin Jiragen Yakin Hukumar

Shugaban Sojin Sama Ya Bayyana Dalilan Da ke Haddasa Hatsarin Jiragen Yakin Hukumar

  • Bayan iftila'in da ya auku na hatsarin jirgin saman sojin Najeriya, shugaban hukumar ya bayyana dalilan da ke haddasa hatsarin jiragen
  • A cewar AM Hassan Abubakar, hatsarin jirgin yana aukuwa ne a dalilin sauyin yanayin da ake samu
  • Shugaban hukumat ya sha alwashin cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen cigaba da kai hare-hare kan ƴan bindiga

FCT, Abuja - Shugaban hukumar sojojin saman Najeriya, AM Hassan Abubakar, ya yi ƙarin haske kan dalilin hatsarin da yake ritsa wa da jiragen saman yaƙin rundunar ciki har da wanda ya auku a jihar Neja.

Abubakar ya kuma sha alwashin cewa dakarun sojojin saman da ke a aitsayen 'Operation Hadarin Daji' da 'Operation Whirl Punch' waɗanda ke kwantar da tarzoma a jihar Neja da yankin Arewa maso Yamma, za su ci gaba da murƙushe ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Harin 'Yan Bindiga: Gwamnan Jihar Neja Ya Sanya Labule Da Shugaban Hukumar Sojojin Saman Najeriya, Bayanai Sun Fito

Shugaban NAF ya bayyana dalilin hatsarin jiragen saman NAF
Shugaban hukumar sojin saman Najeriya AM Hassan Abubakar Hoto: @NigAirforce
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne a hedikwatar hukumar NAF da ke a birnin Abuja, lokacin da gwamnan jihar Neja, Mohammed Umarru Bago, ya kai masa ziyarar ta'aziyyar matuƙan jirgi da wasu sojoji da suka rasa ransu.

Dalilin hatsarin jiragen saman NAF

Shugaban hukumar ya ɗora alhakin hatsarin jirgin kan sauyin yanayin da aka samu, wanda hakan yana dakushe ƙarfin kai hare-hare na jami'an hukumar, cewar rahoton Daily Trust.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Muna da ƙalubale waɗanda suka danganci yanayi. Misali yanzu lokacin damina akwai girgije wanda yakan kare abin da za mu iya gani wajen kai hare-hare."
"Haka kuma, idan lokacin hunturu ya zo, shi ma yana taɓa yanayin ayyukan mu. Waɗannnan su ne ƙalubalen da mu ke fuskanta, sannan muna fatan za ku fahimta idan ayyukan mu sun ɗan yi baya a dalilin wasu daga cikin kalubalen da mu ke fuskanta."

Kara karanta wannan

Jami'an Hukumar Kwastam Sun Kama Harsasai 1,245 Da Aka Boye Cikin Buhunan Shinkafa 'Yar Waje

Abubakar ya bayyana cewa idan dai har jiragen za su ci gaba da shawagi domin farmakar ƴan ta'adda, hatsari zai iya aukuwa, inda ya ƙara da cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne a tabbatar an rage yawaitar aukuwar matsalar.

Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Fado a Neja

A wani labarin kuma kun ji cewa, jirgin sojojin saman Najeriya mai saukar ungulu ya yi hatsari a jihar Neja.

Jirgin saman ya gamu da hatsarin ne a ƙauyen Chukuba na jihar Neja lokacin da yake jigilar mutane zuwa jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng