Masanin Tsaro Ya Ce Sarakuna, Jami’an Tsaro, Dillalan Kwayoyi Da Likitoci Na Da Hannun a Ta'addanci

Masanin Tsaro Ya Ce Sarakuna, Jami’an Tsaro, Dillalan Kwayoyi Da Likitoci Na Da Hannun a Ta'addanci

  • Wani masanin tsaro Sani Shinkafi, ya yi tsokaci dangane da ta'addancin da ke faruwa a jihar Zamfara
  • Ya ce wani abu ne da wasu mutane suka shirya kuma suke amfana da shi
  • Ya ce akwai masu riƙe da sarautun gargajiya, jami'an tsaro, dillalan ƙwayoyi da likitoci a ciki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gusau Jihar Zamfara - Sani Shinkafi, tsohon shugaban kwamitin tuhumar ‘yan bindiga da sauran masu laifuka na jihar Zamfara, ya bayyana masu hannu a ta’addanci a Najeriya.

Ya bayyana ta'addancin da ke faruwa a matsayin wani shiri da sarakunan gargajiya, jami’an tsaro, dillalan miyagun ƙwayoyi da likitoci ke da hannu a ciki kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Sani Shinkafi ya bayyana masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Zamfara
Sani Shinkafi ya bayyana rukunin mutanen da ke da hannu a ta'addancin Zamfara. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Yadda Ta'addanci ke ƙara ƙamari a Zamfara, Shinkafi ya yi bayani

Shinkafi ya ce 'yan ta'addan da suka addabi jihar Zamfara na da makamai da suka fi na duka jami'an tsaron da ke jihar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Ta'addan Jeji Sun Halaka Sojoji 20 a Wani Hari Na Kwanton Ɓauna a Jihar Arewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ƙara da cewa harkar ta'addanci ta zama kasuwanci a wurin wasu mutanen, inda a yanzu haka akwai sama da ƙauyaku 400 da ke ƙarƙashin ikon 'yan ta'adda.

Shinkafi ya kuma alaƙanta ta'azzara da matsalolin tsaron suka yi da rashin samun cikakkiyar kariyar kan iyakoki da jihohin da suka haɗa iyaka da Zamfara.

Shinkafi ya nemi jami'an tsaro su zage damtse kan ta'addancin na Zamfara

Sani Shinkafi ya yi kira ga shugaban ƙasa da ya kawo ɗauki na jami'an tsaro a kan hanyoyin Gusau zuwa Dansadau, Gusau zuwa Sokoto, da kuma Gusau zuwa Shinkafi.

Ya bayyana hanyoyi a matsayin masu haɗari, inda ya nemi sabbin shugabannin tsaro da su zage damtse sosai wajen yaƙar 'yan ta'addan da ke yankin ta hanyar amfani da manyan makamai.

A cikin rahoton na Daily Trust, Shinkafi ya ce baya goyon bayan sulhu da 'yan ta'adda kamar yadda Ahmad Yariman Bakura ya nema, inda ya ce hakan ɓata lokaci ne saboda rashin alƙibilar 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Jami'an Hukumar Kwastam Sun Kama Harsasai 1,245 Da Aka Boye Cikin Buhunan Shinkafa 'Yar Waje

Babban hafsan sojin Najeriya ya ce za su fara farmakar 'yan ta'adda

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan tabbatacin da shugaban sojojin Najeriya, Taoreed Lagbaja ya bai wa gwamnan Zamfara kan matsalar tsaro a jihar.

Lagbaja ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba jami'ansu za su fara kai wa 'yan ta'addan farmaki ba ƙaƙƙautawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng