Yan ta’adda sun tura wakilan su a zaman sulhu da akayi a Zamfara

Yan ta’adda sun tura wakilan su a zaman sulhu da akayi a Zamfara

-A jiya Talata 2 ga watan Yuli 2019, wakilan kwamandojin yan ta'addan Zamfara suka zauna da gwamnatin jihar don a tattauna batun yin sulhu

-Ganawar ta samu halartar manyan masu ruwa da tsaki, ciki hada gwamnan jihar da kuma komishinan yan sanda na jihar

-An kuma bayyana cewa yan ta'addan sun ba da sako kuma za a mika sakon gaba ga wadanda ya dace

Kwamandojin yan ta’adda daga sansani daba daban sun tura wakilansu a zaman sulhu da akayi a Zamafara a jiya Talata 2 ga watan Yuli 2019.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Mutawalle ya samu halartar zaman sulhu tare da komishinan yan sanda na jihar Usman Nagoggo, shugabannin hukumomin tsaro, shugabannin Fulani, shugabannin yan kungiyar tsaro ta sa kai da sauran masu ruwa da tsaki.

Shugaban kungiyar makiyaya na Miyetti Allah, Alhaji Muhammad Kiruwa ya ce “Wakilan yan ta’addan sun zo da sako. Bayan wannan tattaunawa, za mu zauna da komishinan yan sanda don mu mika sakon nasu zuwa gaba sa’annan kuma mu mai do masu da amsar da aka bayar.”

KARANTA WANNAN: Manyan kasa sun ce an shiga cikin halin rashin tsari da hargowa a Najeriya

Kiruwa ya kara da cewa sauran mutanen da suka shirya zaman sasancion na kan hanyarsu ta zuwa jihar don su gana da yan ta’addan a wajajen fakewarsu don su mika masu sakon sasancin da zaman lafiya.

Ya bayyana cewa inde ana so zaman lafiya ya dore, to dole sai an tabbatar da kowa ya ajiye makamansa hadda yan kungiyoyin tsaro na sa kai da yan ta’addan dake boye a daji.

Sakataren yan kungiyar tsaro ta sa kai, Sani Babbar Doka, ya amsa cewa tabbas an kashe Fulani dayawa a kasuwanni da kauyuka ba a kan ka’ida ba.

“Ina mai tabbatar maka, babu wani bafulatani da za a sake kashewa ba akan ka’ida ba a ko ina. Zamu bi sharudda da ka’idojin da aka zartar a wannan zaman sasancin. Amma yan ta’addan dole su daina kai hari kuma su ajiye makamansu.” A cewarshi.

Komishinan yan sandan jihar, ya bayyana cewa yanzu Fulani na zuwa kasuwannin kauyuka ba tare da wata tsangwama ba kuma ya bayyana cewa an matukar samu ragin hare haren da ake kaiwa.

Gwamna Matawalle ya bayyana cewa kwanan nan za a sake samarwa da fulani wajajen zama da kiwo na ruga a duka yankuna uku na jihar.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel