Tinubu Ya Tabbatar Wa 'Yan Najeriya Cewa Ba Zai Kara Kudin Mai Ba

Tinubu Ya Tabbatar Wa 'Yan Najeriya Cewa Ba Zai Kara Kudin Mai Ba

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa ba zai kara kudin mai ba kamar yadda ake yadawa
  • Shugaban ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa, Ajuri Ngelale inda ya ce a yanzu kam babu batun karin kudin mai a kasar
  • Ngelale ya ce a yau dinnan ya samu zantawa da shugaban musamman a kan matsalolin man fetur inda ya ba shi tabbacin hakan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa babu batun karin kudin mai a kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa, Ajuri Ngelale inda ya ce a yanzu babu wannan batu kamar yadda ake yadawa.

Tinubu ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa babu maganar karin kudin mai
Shugaba Bola Tinubu Ya Ba Da Tabbacin Cewa Babu Maganar Karin Kudin Mai. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Me Tinubu ya ce game da karin kudin mai?

Ngelale ya ce ya zauna da Shugaba Tinubu inda ya ba shi tabbacin cewa ba za su kara kudin mai ba, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Na samu zama da Shugaba Bola Tinubu a kan batun man fetur da ya shafi samarwa da kuma bukatun mutane a kan mai din.
"Tinubu na farin cikin sanar da ku cewa kamar yadda kamfanin NNPC ya sanar babu batun karin kudin mai din ko ina a kasar."

Wani tabbaci Tinubu ya bayar a kan mai din?

Ngelale ya kara da cewa kamar yadda Channels TV ta tattaro:

"Mun kara tabbatar muku cewa babu maganar karin kudin litar mai a kasar baki daya.
"Shugaban zai ci gaba da tabbatar da cewa an samu gasa a tsakanin dillalan mai din don wadatuwarsa."

Ngelale ya kara da cewa kamar yadda a baya aka sanar kasuwar man fetur ita za ta na yanke farashin mai din.

Ya ce ba za su dawo baya ba daga wannan tsarin na barin farashin a hannun 'yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zauna da Gwamnan CBN Sakamakon Tsinkewar Farashin Dala a Kasuwa

NNPC Ya Karyata Karin Kudin Mai A Najeriya

A wani labarin, kamfanin mai na NNPC ya musanta cewa zai kara farashin litar mai a kasar baki daya, ya ce wannan magana ba ta da tushe bare makama.

Kamfanin ya bayyana haka ne yayin da ake ta jita-jita a kasar cewa kamfanin na shirin kara farashin litar mai din daga N620 zuwa N720 a kanki wace lita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.