Kotu Ta Daure Ma’aikacin JAMB Watanni 6 Kan Zargin Satar Kwamfuta Don Biyan Kudin Haya A Abuja

Kotu Ta Daure Ma’aikacin JAMB Watanni 6 Kan Zargin Satar Kwamfuta Don Biyan Kudin Haya A Abuja

  • Wani ma'aikacin Hukumar JAMB ya saci kwamfuta a ofishinsu da ke Abuja don biyan kudin haya
  • Kotun majistare da ke Abuja ta yanke masa hukuncin daurin watanni shida ko biyan tara na Naira dubu biyar
  • Yayin bincike, an gano inda wanda ake zargin ya boye Laptop din a gidan kanwarsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kotu ta daure wani ma'aikacin Hukumar JAMB bisa zargin satar kwamfuta a ofishinsu da ke Abuja.

Wanda ake zargin ya kasance mai shara ne a hukumar inda kotun ta yanke masa daurin watanni shida ko biyan tara na Naira dubu biyar, Legit.ng ta tattaro.

Kotu ta daure ma'aikacin JAMB kan satar kwamfuta don biyan kudin haya
Hukumar JAMB Ta Mika Ma’aikacinta Kan Zargin Satar Kwamfuta. Hoto: UGC.
Asali: UGC

Wani hukunci kotun ta yanke kan ma'aikacin JAMB?

An yanke hukuncin ne a kotun majistare ta 2 da ke Kado a birnin Abuja a ranar Litinin 14 ga watan Agusta, kamar yadda rahoton hukumar ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Wata Mata Za Ta Fuskanci Fushin Kotu Kan Kai Wa 'Yan Sanda Tsegumin Karya, Kotu Ta Yi Hukunci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin hukumar, Fabian Benjamin ya ce wanda ake zargin ya tabbatar da satar kwamfutar din kirar HP da ta kai N350,000 a ranar Alhamis 13 ga watan Yuli.

Wanda ake zargin, Emmanuel Odey ya ce ya saci kwamfutar ce don biyan kudin haya na gidansa, cewar Punch.

Me hukumar JAMB ta ce?

Rahoton hukumar na cewa:

"Odey mai shara ne a ofishin JAMB na Abuja, ya fashe da kuka a gaban kotu tare da tabbatar da cewa ya saci kwamfutar don biyan kudin haya.
"Yayin da ya ke neman a yi masa hukunci mai sauki ya ce shi kadai ya yi tunanin haka amma shaidan ne ya saka shi, ya roki a bashi dama ta biyu."

Alkalin kotun, Egbe Joshua ya ce wannan shi ne karon farko na aikata hakan ga Odey kuma bai bata wa kotu lokaci ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zauna da Gwamnan CBN Sakamakon Tsinkewar Farashin Dala a Kasuwa

A dalilin haka, kotu ta ba shi daman biyan kudin tara madadin zuwa gidan kaso, Independent ta tattaro.

A Karshe, Mmesoma Ta Ba Da Hakuri Ga Hukumar JAMB

A wani labarin, dalibar da ake zargi da kirkirar sakamakon jarrabawa, Mmesoma Ejikeme ta gurfana a gaban Hukumar JAMB.

Mmesoma ta karanto takardar ba da hakuri ga hukumar da ma sauran al'ummar Najeriya kan abin da ta aikata.

Ana zargin Mmesoma ta sauya sakamakon jarrabawrta ta JAMB da karin maki don samun gurbin karatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.