Tseguntawa 'Yan Sanda Labarin Karya Ya Jefa Wata Mata Cikin 'Matsala' A Legas

Tseguntawa 'Yan Sanda Labarin Karya Ya Jefa Wata Mata Cikin 'Matsala' A Legas

  • Jami’an ‘yan sanda sun gurfanar da wata a gaban kotun majistare da ke Legas kan zargin ba da bayanan karya ga hukumar
  • Wacce ake zargin, Blessing Udoh mai shekaru 21 ta ba wa jami’an bayanai na karya a kan zargin kisan kai wanda ya tabbata karya ne
  • Mai shari’a, Adeola Olatunbosun ta ba da belin matar a kan kudi Naira miliyan biyu tare da dage sauraran karar zuwa watan Nuwamba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas – An gurfanar da wata mata a gaban kotun majistare da ke Yaba a jihar Legas kan zargin ba da bayanan karya ga ‘yan sanda.

Wacce ake zargin mai suna Blessing Udoh ta ba da bayanai marasa tushe ga ‘yan sanda yayin binciken kisan kai.

'Yan sanda sun maka mata a kotu kan bayanan karya na kisa
Rundunar 'Yan Sanda Ta Maka Mata A Kotu Kan Ba Ta Bayanan Karya Na Kisa. Hoto: Linda Ikeji.
Asali: UGC

Meye 'yan sanda su ka ce wa kotun?

‘Yan sandan sun gabatar da matar a gaban mai shari’a, Adeola Olatunbosun kan tuhume-tuhume guda biyu da suka hada da yaudara da kuma ba da bayanan karya.

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matar mai shekaru 21 ta fadawa ‘yan sanda cewa wani Christopher Ibekwe ya kashe Moses Chidi inda ya tunkuda shi a cikin kogi.

Yayin binciken, ‘yan sanda sun gano cewa bayanan da ta bayar karya ne zalla babu kamshin gaskiya, Linda Ikeji ta tattaro.

‘Yar sanda mai gabatar da kara, Ritah Momoh ta fadawa kotu cewa wanda ake zargin ta aikata laifin ne a ranar 3 ga watan Nuwamba a yankin Agboju da ke Legas.

Wani hukunci kotun ta yanke kan korafin 'yan sandan?

Momoh ta ce aikata hakan ya sabawa dokar kasa sashe na 411 a 95 na kundin laifuka da hukunci na jihar Legas na shekarar 2015, cewar Punch.

Har ila yau, wacce ake zargi, Blessing Udoh ba ta amince da laifukan da ake tuhumarta ba, Tori News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: An Fadawa Tinubu Abu Daya Tak Da Zai Yi Don Shawo Kan Matsalar Tsaro A Jihar Arewa, Ta Nemi Bukata

Mai shari’a, Adeola Olatunbosun ta ba da belin ta a kan kudi Naira miliyan biyu da kuma kawo wanda zai zaya mata a kai.

Ta kuma dage ci gaba da sauraran karar har zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba don yanke hukunci.

Kotu Ta Daure Mata Kan Cizon Mai Musu Sulhu

A wani labarin, kotun da ke zamanta a Kado cikin birnin Abuja ta daure mata mai suna Chioma Okeke kan zargin gaftara wa wata mata mai musu sulhu cizo.

Chioma ta danna wa matar mai suna Roseline cizo bayan ta yi kokarin shiga tsakani a shagonta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.