Gidajen Mai Sun Rufe a Wata Jiha Yayin Da Ake Fargabar Tashin Kudin Fetur Zuwa N1000 Kowace Lita

Gidajen Mai Sun Rufe a Wata Jiha Yayin Da Ake Fargabar Tashin Kudin Fetur Zuwa N1000 Kowace Lita

  • Gidajen mai sun fara rufewa bayan jita-jitan cewa ana iya kara farashin man fetur a yan kwanaki masu zuwa
  • Masu ababen hawa sun bayyana cewa sun gaza samun man fetun a wasu gidajen mai da ke fadin Lagas
  • A halin da ake ciki, gidajen man da suka bude kuma suna fama da layuka masu tsawo ma masu motoci da ke son siyan mai

A jihar Lagas, manyan dillalan man fetur da masu zaman kansu sun rufe wuraren siyar da mansu saboda rade-radin da ake yi game da shirin kara farashin man fetur.

A cewar majiyamu, yawancin gidajen mai sun rufe, sannan wadanda suke bude suna fama da cunkoson ababen hawa da suka yi layi domin siyan mai.

An fara wahalar mai saboda fargabar kara farashi
Gidajen Mai Sun Rufe a Wata Jiha Yayin Da Ake Fargabar Tashin Kudin Fetur Zuwa N1000 Kowace Lita Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Wannan ci gaban ya biyo bayan jita-jitan da ke yawo game da cewar ana iya kara farashin man fetur ya kai har naira 1000 kan ko wace lita bayan kamfanin yan kasuwar mai wato IPMAN ta yi karin haske cewa za a samu sauyi a farashin man fetur a kasar.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

Za a kara farashin man fetur

Masu ababen hawa sun bayyana cewa sun gaza samun mai tunda gidajen mai da dama a jihar sun ki yin aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin da ake ciki, hukumar NMDPRA ta ce yan kasuwar mai sun fara shigo da fetur cikin kasar kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

A baya hukumar NNPCL ce kadai ke da alhakin shigo da kayan har sai zuwa yanzu da abun ya sauya.

Farouk Ahmed, babban jami'in hukumar NMDPRA, ya bayyana cewa daga cikin kamfanonin yan kasuwar mai 56 da suka nemi lasisi, 10 sun nuna jajircewa a kan aiki, yayin da uku suka shigo da mai cikin kasar.

A.Y. Shafa, Prudent, da Emadeb sune kamfanoni uku da Ahmed ya bayyana a matsayin masu shigo da kaya. Ya kuma bayyana cewa karin kamfanoni za su shigo da su cikin makonni masu zuwa.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Legit.ng ta tuntubi wani mazaunin yankin Agege don jin ta bakinsa, inda Malam Hassan Abdullahi ya tabbatar da lamarin.

Hassan ya ce:

“Gidajen mai da dama a hanyar zuwa filin jirgin sama na Ikeja duk sun rufe, sannan yan kadan da suke bude cike suke da layi. Ko dazu da na shiga mota na ji direban na korafi wai an ce masu kudin mai zai kai N800 don haka za su kara kudin mota.”

NNPC ya karyata rade-radin kara farashin man fetur

A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya jaddada cewar baya da niyar Kara farashin man fetur.

Kamfanin na NNPC a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter ya yi watsi da rahotannin kafofin watsa labarai cewa farashin man fetur zai karu zuwa tsakanin N680 da N750 kan kowace lita daya a makonni masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng